Har yanzu na ɗauki kai na a mawaƙi, inji jarumi Auwal Ishaq (Yawale Ɗankurma)

AUWAL Ishaq, jarumin Kannywood wanda ake kira Yawale Ɗankurma a shirin dirama na ‘Kwana Casa’in’, ya bayyana cewa duk da yake ya shahara a fagen aktin, har yanzu ya na kallon kan sa ne a matsayin mawaƙi.

A tattaunawar da ya yi da mujallar Fim, Auwal, wanda asali mawaƙi ne, ya yi nuni da cewa ya samu shahara a fim tun daga lokacin da ya fara fitowa a cikin finafinan Adam A. Zango, wanda shi ne ya fara saka shi a fim. Idan aka samu rol na barkwanci sai a saka shi.

Ya ce daga baya ne ya samu shiga shirin ‘Kwana Casa’in’ inda ya ke fitowa a matsayin Yawale Ɗankurma.

Ya ce: “Amma gaskiya duk da sunan da na yi a cikin shirin ‘Kwana Casa’in’, a yanzu na fi ɗaukar kai na a matsayin mawaƙi.”

To me ya sa haka? Auwal ya ce: “Shi fim sa kai ne, saboda ni duk abin da na sa kai na zan yi sai ka ga Allah ya taimake ni na yi nasara. Shi ya sa ma ko da na fara aktin ban ji cewa ba zan iya ba.”

Ya ci gaba da cewa, “Amma ita harkar waƙa zan iya cewa na gada ne, domin mahaifi na makaɗi ne. Don haka idan ana gadon waƙa, to ni na gaje ta ne a wajen mahaifi na.”

Da mu ka tambaye shi game da ɗaukakar da ya samu kuwa cewa ya yi: “Ai harkar fim ta fi ɗaukaka ni, musamman a shirin ‘Kwana Casa’in’. Duk inda na je zan ji ana ga Yawale Ɗankurma ko a ce saurayin Rayya. Kuma a dalilin sunan da na yi a harkar fim na je ƙasashen Kamaru da Chadi da Ghana da Nijar, da kuma manyan garuruwan ƙasar nan. To alhamdu lillahi, mu na godiya ga Allah.

“Kuma mu na fatan ɗaukakar da mu ka samu ta kai mu ga gamawa lafiya.”