Fitaccen mawaki kuma jarumi a cikin masana’antar Kannywood wanda ya sami lambobin yabo da dama.
Mawakin yayi wani tsokaci a shafukan sa na sada zumunta a inda ya bayyana kamar haka:
Ba Almajirai ne yayan da Iyayen su suka haifa suka kasa kula dasu ba,Idan kana neman yayan da Iyayen su suka kasa kula dasu ,to ka taho masana’antar Film!
Sannan ya kara da fadin haka:
Wannan shine gaskiya Malamai,ko tayi dadi ko kar tayi muku dadi,Kowa ya dakko Sharrin sa sai kan Almajirai da iyayen su???,to mu munsan abunda kuke kira da Almajirci duk da ba sunan sa kenan ba,munsan niyyar dake saka iyaye su kai yayan su ,mun kuma ga amfaninsa,wato kunfi son a bar yara a Daji aita basu bindiga suna kashe mu wannan shine burin ku?? Wannan shine kawai.
Ayi hakuri damu!
A cewar Naziru Sarkin Waka,sai masu bibiyar abubuwan dake faruwa,sunce hakan yana da nasaba da abunda Jaruma Nafisat Abdullahi ta fito ta fada akan iyayen da suke haifar yara suna kasa kula dasu.
Shin mene ra’ayin ku akan wallafar jaruman biyu,Nafisa da kuma Naziru.
Hotunan Nafisat Abdullahi da Naziru Sarkin Waka:
Leave a Reply