Kamar dai yanda muka yi bayani a wasu lokuta a baya, Dabino nada matukar amfani wajen magance cututtuka masu yawan gaskeda kuma inganta lafiyar jikin dan adam, haka Madara domin ita kuma tana dauke da wasu sinadarai masu mushimmanci.

Idan aka hada dabino da madara waje daya to sai a nika su duka sinadarai ne dake a tsakanin Dabino da madara wadanda suke da karfi, da suke amfanar da jikinmu.
Idan kanason karin ruwan maniyyi domin biyawa iyalun ka bukata a lokacin jima’i to kayi Wannan hadin, na Dabino da Madara.
Za’a nemi dabino mai laushi misalin rabin karamin gwanganin sai a cire kwallayen cikin Dabinon a zuba ruwan zafi a karamin kofi sai a bari ya kwana a ciki.
Sai da safe a tace ruwan a fasa gwangwanin Madara Peak Milk a gauraya rabinsa da ruwan dabino, yana da dandanon gaske kada a yawaita Madara tafi ruwan Dabinon yawa kuma kada a dai-daita yawan su, concentration din zai yi yawa kada a saka suga kada a saka zuma a ciki.
Mai ciwon sugar kada ya sha wannan hadin maganjn, wanda madara ke saurin burkucewa ciki sai ya sanya kadan.
Shi amfanin wannan hadin bama iya ruwan maniyyi yake karawa ba kawai, yana kara abubuwa da dama a jikin Namiji kamar haka.
(1) – Yana karawa Namiji yawan ruwan maniyi.
(2) – Yana kara sha’awa a tsakanin ma’aurata Namiji da Mace.
(3) – Yana Kara karfin kwakwalwa da saita tunani, za’a iya hadawa a baiwa yara su sha domin kara karfin basira, haka kuma babba zai iya sha dan samun nutsuwa.
(4) – Yana karawa mata ni’ima.
(5) – Yana kara yawan jini.
(6) – Yana karawa jiki karfi da kuzari.
(7) – yana zama a matsayin multivitamins
maimakon shan su vitamin A ko B ko C ko vitamins na Appetite to a rinka shan wannan hadin za’a ji canji a jiki.
(8) – Wanda ya taso daga jinya zai iya shan wannan hadin matukar baya fama da wata cuta wacce ba’a shamata madara.
(9) – Maganin yawan mantuwa da rikicewar kwakwalwa musamman ga mai fama da wata damuwa haka.
(10) – Namiji mai karamcin sha’awa a jiki shi ma zai iya shan wannan hadin maganin.
(11) – Yana karawa garkuwar jiki karfi da lafiya.
(12) – Yana kara yawan ruwan Nonuwa ga mace mai shayarwa.
Allah yasa mu dace.
