Immigration – Hukumar kula da shige da fice zata dauki ma’aikata 5,000

Hukumar Kula Da Shige Da Fice ‘Immigration’ Zata Ɗauki Ma’aikata 5,000

Mukaddashin Kwanturola-Janar na Hukumar Kula da Shige-da-Fice ta Kasa, NIS, Idris Jere, ya ce ana shirin ɗaukar ƙarin ma’aikata 5,000 a hukumar.

Jere, wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a Dutse a jiya Asabar, ya ce matakin na da nufin magance matsalar karancin ma’aikata a hukumar ta NIS.

“Game da rashin isassun ma’aikata a NIS, kamar yadda kuka sani, yanzu mun kammala ɗaukar ma’aikata kuma muna horar da wadanda aka dauka a halin yanzu.

Kamar yadda kuka sani, gwamnati ta sanya takunkumin daukar ma’aikata, amma ta ɗage hakan a kan hukumomin tsaro, domin tsaro shine mafi muhimmanci.

“Don haka, mun rubuta wa shugaban ƙasa kuma na tabbata za mu samu amincewar ɗaukar karin ma’aikata kusan 5,000 a cikin NIS,” in ji Mista Jere.

Ya kara da cewa ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ya aike da takarda ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ya nuna aniyar sa ta amincewa da bukatar ɗaukar ma’aikatan..