Ina alfahari da cika shekaru 14 da aure ba tare da an ji kanmu matata ba, Jaruma Lawan Ahmad

Fitaccen jarumi kuma furodusa a masana’antar Kannywood, Lawan Ahmad ya bayyana cewa a zamansu da matarsa, Saratu Abdulsalam, babu wani ya taba kai karar wani tsawon shekaru 14 da aure.

Mujallar Fim ta zanta da jarumin inda yace yana matukar farinciki tare da alfahari da cika shekaru 14 a ranar 25 ga watan Oktoban 2022, ba tare da an ji kansa da matarsa ba.

Ya wallafar zazzafan hotonsa tare da uwar ‘ya’yansa don murnar. Yayin tattaunawa da Mujallar Fim, jarumin ya ce:

Alhamdulillah, ina farinciki tare da alfahari da Allah cikin ikonsa yasa mu ka cika shekaru 14 da aure. Kuma babu wani a cikinmu da ya taba kai karar wani gidan iyayensa. Mu na zaune da dadi babu dadi, har mu ka cika shekarun nan.

Tabbas ba karamin abin alfahari ba ne wannan, kuma ba karamar ni’ima bace da Allah yayi mana tsawon shekarun nan. Gaskiya ina matukar farinciki.”

Lawan yana daya daga cikin ‘yan fim wadanda babu wanda ya taba jin wani mummunan labari tsakaninsa da matarsa duk da yadda jama’a ke kallon ‘yan fim ba sa rike aure.

Yayin da aka tambayeshi ko zai yi karin bayani, ya bayyana cewa:

Babu wanda ba ya zaman aure. Dama idan har aka yi aure akwai saki, kuma addini ma ya amince da hakan. Kowa ya riga ya sani. Kuma dalilin da yasa ake ganin kamar ‘yan fim ba sa zaman aure, saboda komai nasu a bude yake.

Ya bayyana cewa da zarar dan fim ya bayyana wani abu ko ya wallafa shi, nan da nan mutane za su dauka su ci gaba da yadawa. Hakan ya biyo bayan yadda kowa ya san su.

An tambayeshi idan yana da burin kara aure, sai ya kada baki yace, “shi aure zuwa yake yi. Don haka babu wani zabi sai abinda Allah ya tabbatar mana.” Yanzu haka yaran da Allah ya azurta su da su guda hudu ne, akwai Ahmad, Aliyu, Fatima da Habiba.