Ina amsa kiran waya sama dubu biyu a rana – Kawu Dan Sarki mai wakar Ingallo

Mawakin nan da tauraruwarsa ke haskawa a ‘yan kwanakin nan, Muhammad Khalid da aka fi sani da ‘Kawu Dan Sarki’ ya ce farkon sana’arsa ita ce kafinta kafin daga bisani ya rikide ya fara waka.

Haifaffen jihar Bauchi, Kawu Dan Sarki a zantawarsa da DCL Hausa ya ce a iya sakandare matakin karatunsa ya tsaya, inda ya ce yanayin jikinsa bai bashi damar ya iya yin wani aikin karfi ba, inda ya ce idan ya fita ya yi sana’ar kafinta a rana, ya samo kudin da ba su kai Naira dubu biyu ba, kudin za su kare wajen magani, wani lokaci ma har a yi ciko.

“Sanadin fara waka ta shi ne neman kudi, kamar yadda na fadi, aikin karfi ba zan iya ba, abin dai da yawa, amma dai a takaice, ni abin da ya kai ni studio ba waka bace, saboda ina aikin karfi, ina aikin kafinta, in samu dubu daya, amma ta kare a magani, har ma a kara da ciko a gida, wannan shi ya sa na koma studio, in su Naira dari, dari biyu a cikin inuwa.” Inji shi.

Kawu Dan Sarki ya ce bai share wasu shekaru masu yawa a harkar waka ba, sannan ya musanta masu zargin cewa yana saka kalmomin batsa a cikin wakarsa, yace kawai dai yana zurfafa kalamansa su yi kwari a cikin wakokinsa.

Ya shaida wa DCL Hausa cewa yana yin wakoki kala daban-daban, na soyayya, suna, biki, siyasa da sauransu, amma dai ya di karkata a wakokim soyayya.

 

Muhammad Khalid da ya yi wakar nan mai taken “Ingallo Na Ciwo” ya ce yana da burin ya bar baya mai kyau, sannan ya ce yana fatar ya ci lokacinsa, tare da fatar kafa mutane da yawa.

Ya ce a rana yana amsa kiran waya sama da dubu biyu daga masoyansa na sassan duniya daban-daban ya amshi sakonni ta manhajar ‘whasapp’ shi ma ba iyaka da sauran shafukansa na sada zumunta.

 

Da DCL Hausa ta tbaye shi ko wanene ubangidansa a masana’antar Kannywood, sai Kawu Dan Sarki ya ce shi mawaki Dauda Kahutu Rarara ne ubangidansa a industiri, saboda shi ya dauki nauyin bidiyon mafiyawan wakokinsa har duniya ta sanshi.

Yace a kiyasi wakokinsa za su kai 32 a halin da ake ciki da ya ce shi ba ya rubuta waka, kawai idan na bude kidana bana tashi sai na kammala wakata, sai dai in yi ‘yan gyare-gyare idan na kammala.

 

KawuDan Sarki mai kimanin shekaru 28 ya ce babban kalubalen da ke damunsa, shi ne wasu na tunanin girma ne ya kawo haka, ko na tattara manyan kudi, ta yadda zaka ga wani ya kawo maka matsalarsa ta 500,000 amma baka da hali.