Ina goyon bayan Aisha Buhari kan hukuncin da ta dauka akan Yaron da yaci mutuncinta – Mansurah Isah

Abinda wasu mutanen suke yi a soshiya midiya abin Allah wadai ne, ni ba shugaba bace kuma ba matar shugaban kasa bace, amma a matsayina na yar film abin yana cimana tuwo a kwarya idan wasu mutane marasa tarbiyya, marasa kunya, mahaukatan mutane da ba su sanin darajar mutum suke shiga shafukan soshiyal midiya suna cin zarafin mu.

Abin yana damun mu sosai saboda baka sanin wanda yake yin hakan domin wasu za su bude account ne da sunan mutum sai su dinga yin abubuwan da ba su dace ba suna fadin labaran karya akan mu suna cin mutincin mu.

A wani rubutu da ta wallafa a shafinta na instagram Jarumar ta ce, “Kada wanda ya tambaye ni in ce wani abu a kan A’isha Buhari. Ni ma na taɓa shiga wannan halin. Haka ‘ya ta ma ta taɓa shiga irin wannan halin. Na ce a’a da cin mutuncin soshiyal midiya da kalaman ƙiyayya.”

Idan abin ya faru wasu lokuta mu yi kuka a fili ko a ɓoye. Manyan jaruman duniya da ba za su iya ɗaukar hakan ba, su kan kashe kan su.

Amma ni ba zan kashe kai na ba, sai dai ba zan taɓa barin wanda ba shi da tarbiyyar gida ya yi wasa da rayuwa ta ko lafiya ta ba. Za su yi basaja da sunan ka, su ɗora bidiyon marasa lafiya a matsayin kai ne.

“Wallahi, wallahi, abin da ciwo, har ta kai  ƙarshe, na kai wasu marasa kunya gidan yari. Ba zan ɗaukar wa kai na ko iyali na ba. Kada ku taɓa ni, shi kenan.” Inji Mansurah.