Jarumar Fina finan shirin wasan hausa na masana’antar kannywood Hauwa Waraka tayi wata sanarwa akan neman mijin aure, da take wanda zasu rufawa juna asiri.
Yayin wata hira da shafin gidan Jaridar BBC HAUSA Jarumar hauwa waraka ta bayyana cewa hakika, tana neman mijin aure amma bazawari wanda yake ya mallaki hankalin kansa.

Wanda zai riketa da amana hannu biyu ba, saurayi wanda yake dan shekara 20 ko shekara 25 Ba, domin tafison namiji bazawari mai mata daya ko biyu.
Sannan ta kara dacewa duk mutumin daya shirya yazo kofa a bude take harma ta kara dacewa zatayi mutumin da yazo auren nata Kayan lefe kyauta, ba sai ya kashe ko sisi ba.
Jarumar Ta mayar da martanin cewa” da Yawan Mutane Dasu Suke Bada Aljanna Da Bazasu Baiwa Dan Fim Ba Saboda Kallon Da Suke Yi Mana, Cewar Jarumar Fina finan Hausan, Hauwa Waraka.
Sannan jarumar tace mafiya yawan mutane suna musu kallon a cikin su akwai mutanan banza, amma gaskiyar lamari idan mutum zai zauna dasu to zai fahimci duk yadda abubuwan suke kasancewa.
Kada ka yankewa mutum hukunci Ba tare da kayi wata kyakkyawar Mu’amula dashi ba saboda hakan ba adalci bane gaskiya domin kuwa zargi a musulunci ma, haramun ne ba kyau yakamata kudaina
Leave a Reply