Inda Ranka Kasha Kallo: Kalli Abinda Wata Budurwa Tayi A Matsayin Murnar Zagayowar Ranar Haihuwa

Kamar yadda kuka sani mutane a wurare da dama suna bijiro da abubuwa daban daban lokutan da suke cikin wani yanayi na farin ciki.

Wannan yasa mutane da dama lokacin bikin zagayowar ranar haihuwarsu suke kirkiro wani abu da zai dauki hankalin mutane.

A wannan lokaci amihad.com taci karo da hotunan wata budurwa wanda tayi bikin zagayowar ranar haihuwarta a cikin baho yayin da mahaifiyarta ta riketa kamar jaririya.

A cikin hotunan zaku ga yadda mahaifiyarta ta nuna yadda takeyi mata wanka daidai da lokacin tana karama sannan ta shafa mata mai.

Kazalika duk cikin hotunan harda wanda ta sanya mata kaya.

Gadai hotunan nan zamu gabatar muku dasu sai ku kalla a kasa.