Innalillahi: An kashe ‘Yan bindiga 8 an kubutar da mutane 6 a wani harin bamabamai da rundunar sojojin saman Najeriya

An kashe ‘Yan bindiga 8 an kubutar da mutane 6 a wani harin bamabamai da rundunar sojojin saman Najeriya

Rundunar ‘yan sanda a Katsina ta ce wani farmaki da aka kai da safiyar Lahadi a maboyar ‘yan bindiga a kauyen Tandama, ya yi sanadin kashe ‘yan bindiga akalla takwas tare da kubutar da wasu mutane shida da aka sace.

Jami’an ‘yan sanda da ke samun goyon bayan rundunar sojin sama, sun kai farmaki kan ‘yan bindigar da ke karamar hukumar Danja a jihar Katsina

Kakakin rundunar ‘yan sandan Gambo Isah ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar cewa an kashe fitattun ‘yan bindigar har da Abdulkarim Faca-faca a harin.

Kalli bidiyon anan:

A wani bangaren kuma za ku ji cewar
An Kashe Shugaban Boko Haram A Borno

Rundunar sojin sama ta Operation Hadin Kai, ta bayyana cewa sun kashe Alhaji Modu, “Shahararren shugaban kungiyar Boko Haram.

A cewar Zagazola Makama, kwararre kan yaki da ta’addanci, Modu, wanda aka fi sani da Bem Bem, an kashe shi tare da wasu mayakan Boko Haram 27 a Borno.

Ya ce an kashe Modu ne a ranar 3 ga watan Agustannan, a wani harin da sojoji suka kai a tsaunin Mandara, karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno.

Lallai wannan ya nuna cewar jami’an tsaronmu sun amshi kiran shugaban kasa muhammadu buhari na su gaggauta yin fatafata da ‘yan ta’adda.

Allah ya taimame su, ya kawo mana karahen zubar da jini a kasar nan.