Wata babbar kotun Shari’ar musulunci dake zamanta a garin jihar Yobe state dake nigeria cikin babban birnin jihar na Damaturu ta yankewa wani mutum hukunci, biyo bayan yadda yayiwa ‘Yar cikinsa fyade.
Kotun dake zamanta a babban birnin jihar na damaturu ta bayyana cewa mutum dan asalin jihar ne ta yobe dake cikin garin na damaturu a jihar.
Alkalin kotun mai shari’a Mohammed Bilyaminu ya yanke hukuncin cewa dukkanin abubuwan da ke cikin sashe na 470 dana 280, na kundin laifuffuka masu gabatar da kara sun tabbatar da su.
Gidan Jaridar Hausa Daily News, ce ta rawaito cewa, yayin da yake karanta shaidar, Alkalin ya bayyana cewa, PW 1, wani sufeton ‘yan sanda, a lokacin da yake ba da shaida, ya tabbatar da cewa mai laifin ya yi lalata da ‘yarsa.
Haka zalika lokuta Da dama, ba tare da amincewarta ba wanda yarinyar ta haihu amma yaron nata, jaririn ya mutu, batare da kowa yasan hakan ba, a cikin ‘yan kwanakin nan da abin ya faru.
Yanzu haka dai kotun ta tisa keyar mutumin da ake zargin da dirkawa ‘yar cikin nasa juna biyu izuwa gidan gyaran hali, batare data san mahaifin nata ne, yayi mata cikin ba har saida bincike yayi tsauri akan wannan lamarin daya faru.
Leave a Reply