Innalillahi Wainna Ilaihi Raji’Un Amarya ta Mutu a Daren Farko Ana Tsakada Shan Soyayya da Mijin ta Yanzu….

Toffa Babbar Magana Amarya ta Mutu Daren Farko Ana Tsakada Shan Soyayya Tsakanin ta da Angon ta.

Ana tsaka da soyewa a daren farkon wasu ma’aurata, ciwon zuciya ya kashe amarya har lahira Masoyan biyu ‘yan asalin kasar Brazil sun yi aure amma a daren farko amarya ta fara alamun rashin lafiya Bayan ango ya kira masu taimakon gaggawa, ana kan hanyar asibiti amarya mai shekaru 18 ta rasu.

Angwancin wata amarya mai shekaru 18 da angonta mai shekaru 29 ya tsinke bayan amarya ta samu ciwon zuciya kuma ta mutu yayin da suke saduwa a daren farko. Kamar yadda The Sun ta ruwaito, amaryar ta fara nuna alamun rashin lafiya kuma ta fadi a gidansu dake garin Ibirite a Brazil a yammacin Alhamis. Ads by.

Lamarin ya faru ne bayan ma’auratan sun yi aure kuma suna wani shagali a gonar mijin, Pulse ta ruwaito.

An gano cewa amaryar ta fara alamun rashin lafiya kuma mijin ya kira makwabtansa domin taimako sannan ya tari direban tasi ya kaita asibiti amma ya ki. Ango ya nemi masu taimakon gaggawa Ya yanke shawarar kiran taimakon gaggawa daga asibiti. Bayan dogon jira an kawo masa taimako daga asibiti kuma sun samu matar tana kokawa da numfashinta, lamarin da yasa suka ce zuciya ce matsalarta.

Amarya ta rasu kan hanyar zuwa asibiti Cike da takaici tare da alhini, ana kan hanyar kai sabuwar amaryar asibiti tace ga garinku An gano musabbabin mutuwar amarya Bayan duba gawarta, babu wata alama ta fada ko wani abu makamnacin hakan, amma wata makwabciyarsu tace bata ji ihu ko wani sauti ba na nuna alamar ma’auratan fada suka yi.

Bayan sake duba gawar an gano cewa amaryar tana da matsala a hanyar numfashinta kuma mutuwa tayi ba kasheta aka yi ba. Angon cike da alhini da dimuwa ya fada bakin ciki sakamakon mutuwar amaryarsa wacce ta kasance masoyiyarsa. Ya ce baya tsammanin zai cigaba da rayuwa a kasar Brazil.

Wannan Kenan Kadan Daga Rahoton Mu Akan Yadda Wannan Amarya ta Rasa Rayuwar ta Allah Sarki.