Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raj’un Anyijana izar Iyalan Mutun 7 Dasuka Rasu Sanadiyar Basu Abinci Mai Guba

Wannan mummunan al’amari dai ya faru ne a wani gari mai suna Danbaza, a wata karamar hukuma a jihar Zamfara.

Rahoton ya nuna a ranar Talata 16 ga watan Agustannan ne wasu da ake tunanin Mata da Miji ne masu yara 6 duka mata suka ci wani dambu mai hade da wasu kayan lambu, inda nan take suka sheka barzahu.

Wata majiya dake kusa da wanda abin ya faru da su wato Mallam Muhammad Kabir ya ce yara hudu suka mutu nan tame yayin da sauran ukun suka rasu bayan da aka garzaya da su asibiti.

Gwamnati tace ta aike da wakilanta zuwa jana’iza tare da jajanta ma yan-uwan mamatan.

Shafin NEWS ALL  na amfani da wannan dama wajen fadakar da al’umma kan kula da abubuwan abinci musamman na kayan lambu da kayan makulashe.

Allah ya raba mu da duniya lafiya.

Source:JanzakiTv.Com