Innalillahi wa’inna illahirraji’un “Na rasa duka ‘ya’yana” – Wani dan Najeriya ya yi alhinin rasuwar ‘ya’yansa guda biyu

wani dan Najeriya na zaman makoki bayan ya rasa ‘ya’yansa guda biyu namiji da mace cikin shekaru uku.

Mahaifin marigayin, Zeeyauhaq Nuhu, a wani sakon da ya wallafa a shafin sada zumunta na yanar gizo yana jimamin rasuwar ‘ya’yansa, ya ce ‘yarsa ta rasu a shekarar 2019, kuma dansa ya rasu ranar Laraba, 26 ga Oktoba, 2022.