Innalillahi Wa’Inna’ilaihi Raji’un Ashe Wannan Shine Dalilin Rasuwar Director Shirin Izzar So

Assalamualaikum warahamatullahi wabarkatuhu barkan ku da sake kasancewa damu a wani sabon rahoto da yake bayyana a yanzu haka

Mun samu labarin gaskiyar abinda ya faru da fitaccen jarumin kannywood nura Mustapha waye wanda ya rasu

Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un Allah yayiwa jarumin kannywood rasuwa director cikin fiim din hausa mai dogon zango wato Izzar so.

Hakika Jarumi kuma director cikin shrin Izzar so wanda akafi sani da Nura mustapha waye mutumin kirki ne kuma ya kasance mai matukar son annabin mu annabi Muhammad (S.A.W) da kuma kwaikwayon halayan sa.

Jarumin ya tafi gidansa da misalin karfe sha biyu na daren ranar asabar lafiya kalau kafin wayewar gari allah ya karbi abinsa ubangiji allah yayi masa gafara allah kuma ya baiwa iyalansa hakurin jure wannan rashi.

Hakika marigayin ya samu kwakkyawar shaida a wurin mutane daban daban sannan ya kasance mutum mai kaunar manzon mu manzon Rahama S.A.W.

Muna matukar godiya da bibiyar mu a kowane lokaci a tashar Mai albarka ta hausablogng