Innalillahi Yadda aka kama Kasurgumin mai garkuwa da mutane da kayan sojoji a Jihar Kano

Wani rahoton da shafin mu ya samu a unguwar Janbulo dake jihar Kano,an sami nasarar kama wani Kasurgumin mai garkuwa da mutane da yake yiwa sojoji sojan gona.

An kama mutumin ne bayan da wata hatsaniya ta faru a unguwar, ƴan Bijilanti sukayi ram da wata yarinya wacce daga baya aka gano yarinyar sa ce.

Kama yarinyar keda wuya aka mikata ofishin Hisbah mafi kusa,bayan an kaita dinne yaje yayi musu barzana da kayan sojoji har takai da yayi harbi ya karbi Yarinyar daga hannun ƴan Hisbah din yankin.

Mutanen unguwar duba da abunda ya faru sai basu yi kasa a gwiwa ba suka kai rahoton shi zuwa ofishin ƴan sanda mafi kusa,bayan sun kai shi din ƴan sandan kamar yadda wani dan unguwar ya sheda yace basuyi wani abu ba akan hakan.

Bahaushe yace daga bakin mai ita tafi dadi,ba tare da bata lokaci ba zaku iya kallon cikakkiyar hirar da wani mai amfani da kafar sadarwa ta Facebook Abubakar Sadiq yayi da dan unguwar.

News All