Innalillahi Za’a Rufe Makabartu a Abuja Matukar Gwamnati Bata Biya Hukumar Kula Da Muhalli Hakkinsu Ba

Ma’aikatan kula da muhalli na Abuja sun yi barazanar rufe maƙabartu da babbar cibiyar jibge bahaya ta birnin, matuƙar hukumomi suka gaza cika alƙawarin fara biyansu da sabon tsarin albashi.

Sun ye barazanar ne bayan ƙungiyarsu ta cimma yarjejeniya da hukumomin Abuja sakamakon yajin aikin gargaɗi da ya kai ga rufe maƙabartar Gudu, kafin buɗe ta daga bisani.

Hukumar kare Muhalli ta Abuja ta ce ana ci gaba da tantance bayanai don ganin an fara biyan ma’aikatan sabon tsarin albashin da aka amince da shi tun a 2019.

Ma’aikatan kula da muhallin na Abuja sun ce za su rufe maƙabartar Gudu da ta Gwarinpa da ofisoshin kare muhalli da tashoshin aikin shara da babbar cibiyar jibgewa da tace bahaya ta Wupa a ƙarshen watan Satumba matuƙar hukumomi suka gaza fara biyansu da sabon tsarin albashi.

Maƙabartun Gudu da na Gwarinpa da ke ƙarƙashin Hukumar kare muhalli ta Abuja, na da matuƙar muhimmanci ga birnin Abuja don kuwa a nan ne ake bizne gawawwakin da ba a san masu su ba.

Na mutanen da suka rasu ta kamar sanadin hatsari da waɗanda aka tsinta, da gawawwakin da makusanta ba su je sun karɓa a asibitoci ba.

Shugaban ƙungiyar ma’aikatan, Mukhtar Bala, ya ce kiraye-kirayen al’umma ne ya sanya su buɗe maƙabartar ta Gudu kafin kawo ƙarshen yajin aikin gargaɗi da suka yi a ranar Alhamis.

Shugaban ƙungiyar ma’aikatan Kwamared Mukhtar Bala ya ce ma’aikatan kula da muhalli na Abuja sun ƙunshi jami’an duba-gari da Jami’an tsaftace birni da ma’aikatan kula da bututan kwashe bahayar Abuja waɗanda suka haɗar da na babbar tashar tace bahaya ta Wupa da jami’an bin diddikin tsarin gine-gine da lauyoyin hukumar da sauransu.