Isra’ila ta sake kashe wani kwamandan gwagwarmya na Falasɗinawa daga ƙungiyar Palestinian Islamic Jihad (PIJ), yayin da adadin waɗanda ta kashe a hare-haren Zirin Gaza ke ƙaruwa.
Yara ƙananana shida da mayaƙan PIJ da dama – ciki har da jagorori Khalid Mansour da Tayseer Jabari – na cikin Falasɗinawa 32 da aka kashe zuwa yanzu.
Makaman roka da mortar kusan 600 ‘yan gwagwarmaya suka harba kan Isra’ila daga Gaza tun daga Juma’a, a cewar wani jami’in gwamnatin yankin.
Wannan ne tashin hankali mafi girma tsakanin ɓangarorin biyu tun wanda aka yi na kwana 11 a watan Mayun 2021, wanda ya yi sanadiyyar kashe Falasɗinawa fiye da 200 da kuma Isra’ilawa kusan 12.
Jami’an Isra’ilar na gargaɗin cewa hare-haren da take kaiwa za su ɗauki tsawon mako ɗaya.
A ranar Lahadi, makamin roka da Falasɗinawa ke harbawa sun kai Birnin Ƙudus a karon farko tun yaƙin 2021.
Leave a Reply