Jama’ar Gari Sunkori Wani Mutum Tare Da Yar sa Bayan Yayi Lalata Da ita Har Tasamu juna 2

Jama’an sun kori wani mutum daga garinsu bayan ganin ya koma zaman lalata da diyarsa ta cikinsa bayan an tambayeta kuma ta bayyana gaskiya, LIB ta ruwaito.Dama tun farko an kori Amaechi Agnalasi da diyarsa, Queen Bassey daga garin Nnobi da ke jihar Anambra bayan gano su na lalata da juna har sun haifi yara biyu.Ta bayyana yadda mahaifinta ya dinga lalata da ita kuma ya sanya ta tayi alkawarin ba za ta sake kula wani ba sai shi.Yayin da ake titsiye shi don ayi masa tambayoyi, Amaechi ya ce ya tilasta diyarsa ta yi masa rantsuwa saboda ba ya so ta bar shi.Ya ce sauran yaransa sun tsere, hakan yasa ya yi hakan don kada Queen ta bar sa ya fara lalata ta ta.Ga bidiyon mutumin yayin yake fadin hujjarsa ta yin hakan: