Fitacciyar jaruma Surayya Aminu wacce aka fi sani da Rayya a cikin shirin Kwana Casa’in mai dogon zango ta kammala karatunta a makarantar jami’a. Kamar yadda rahotanni su ka nuna, ko da take shirin fim din, hakan bai karkatar da ita daga karatunta ba, sai da ta zage damtse ta kammala.
Jarumar ta wallafa hotunanta a shafinta na Instagram @Rayya_90days cike da farinciki yayin da ta gama rubuta jarabawar karshe da abokan karatunta sanye da farar riga wacce aka yi mata rubutu kala daban-daban a jikinta wanda ake kira da “
Nan da nan masoyanta da masu yi mata fatan alkhairi su ka dinga kora mata addu’o’i na fatan alkhairi yayin da wasu su ka dinga mamakin ganin yadda ta hada karatu da sana’ar fim a lokaci guda.
Da alamu Foliteknik din Jihar Kano ta kammala don kowa ya san a halin yanzu jami’o’in gwamnati basu dade da komawa yajin aiki ba, yayin da na kudi kuma ba yanzu bane lokacin gamawarsu.
Sannan a shafin nata ta bayyana cewa a Kano ne ta kammala karatun wanda duk wanda ya ke da labari zai gane cewa ‘yan foliteknik ne suke gama karatu yanzu. Muna mata fatan alkhairi tare da addu’ar Allah ya kawo babban rabo.
Ba Rayya bace kadai jarumar Kannywood wacce take hada sana’arta da fim ba. Jarumai kamar Maryam Booth, Rahma Sadau da sauransu ma sun ci gaba da karatu kuma sun kammala lafiya lau.
Jarumai kuwa kamar Nafisat Abdullahi da Rahama Hassan sai da su ka kammala karatu su ka shiga masana’antar.
Leave a Reply