Jarumar shirin Kwana Casa’in Surayya Aminu tayi nasarar samin shiga gidan BBNaija

Jarumar shirin Kwana Casa’in 90 “Surayya Aminu” ta halarci tantancewar shiga gidan BBNaija kuma har sun amince da ita tare da tura mata gayyata.

Kamar yadda ta bayyana ta sami gayyatar amma bata duba Email din ta ba har aka gama rijista.

lamarin da bata ji dadin sa ba ko kadan sanannen abu ne cewa, mabiya addinai a
Najeriya da duk wanda ya san mutuncin kansa, yana sukar shirin ganin irin bada kalar da ake zubawa a cikinsa.

Kiris ya rage ma’abota kallo suga jaruma fim mai dogon zango na Kwana Casain, jaruma Surayya Aminu, tsamo-tsamo a cikin shirin BBnaija na wannan shekarar.

Wannan shirin dai yafi farin jini ga ‘yan kudancin Najeriya kuma hatta mabiya addinin Kirista suna kira ga mabiyansu da su nisanci shirin sakamakon tsagwaron ba dala da ake nunawa.

Har ila yau, a shirin babu zancen addini domin babu masallaci ko coci na tsawon watanni uku zuwa hudu, inda ake cigaba da shirin ana zabe tare da zare mutane.

Daga bisani, wanda ya zama zakaran gwajin dafin shirin na tafiya da manyan kyautuka kamar miliyan dari mota da sauransu.

A wallafar da jaruma Rayya tayi a shafukanta na instagram da TikTok, ta bayyana sakon da mashiryan shirin suka turo mata bayan ta shiga tantancewar shirin har ta samu nasara.

Sai dai kash, rashin duba sakonninta na Email yasa bata ga gayyatar da suka turo mata ba sai daga bisani.