Jarumar wasan Talabijin ta kasar Faransa “Marin El Himer” ta karbi addinin Musulinci

Wata fitacciyar jarumar wasan talabijin na musamman ‘yar kasar Faransa mai suna Marin El Himer ta karbi addinin musulunci, inda kuma ta bayyana cewa wadannan kwanaki data karbi musulunci.

Kwana biyu bayan da ta karbi addinin Musulunci “Eli Himer” ta dora wasu hotuna nata a shafinta na sada zumunta instagram sanye cikin hijabi a kusa da dakin ka’aba, guri mafi tsarki a musulunci.

Ta bayyana tsananin matukar farın cikin ta da wannan babban abu da ya sameta na karbar addinin musulunci, domin tana fatan ta samu rayuwa mai kyau da zata cigaba dayi mata jagora har karshen rayuwar ta, kamar yadda “Labarun Hausa” suka wallafa.

In sha Allah, bani da wasu kalmomi isassu da zasu iya bayyana irin tsananin murnar da zakuwa da nake a ciki a wannan yanayi.

Tafiya ce wacce nake fatan zata dora ni akan madaidaiciyar hanya kuma ta taimaki rayuwa ta in Sha Allahu.

Babu wasu isassun kalmomi da zan iya bayyana irin matukar farin cikin da nake ciki a wannan lokaci, a cewar EliHimer.

Ta ce, wannan mataki da ta dauka na komawa addinin musulunci tayi shi ne bisa tunanin ta da zuciyar ta da kanta.

Tana fitowa a shirin na musamman a Faransa jarumar dai ta kasance tana fitowa a cikin shirin talabijin na musamman na kasar Faransa mai taken ‘yarima da sarauniyar kauna.

Masoya da magoya bayan ta ma bata mance da su ba inda sai da ta gode musu bisa kyautatawa da kuma goyan bayan da suka bayar.

Kamar yadda wata jaridar kasar Faransa ta wallafa, Himer ta girma ne a wajen dan uwan baban ta, ta dauki tsawon lokaci tana bincike akan inda ainihin baban nata yake, cikin wannan binciken nata ne ta karbi addinin musulunci.