Jerin matan kannywood guda 8 wadanda ake zargin sunyi bilitin bayan samin daukakar su a harkar fim

A cikin wannan labarin zamu kawo muku sunaye hotuna da kuma takaitaccen bayani dangane da jaruman Kannywood mata guda takwas (8) da ake zarginsu da sauya launin fatarsu bayan samun daukaka a fim, kamar yadda shafin “Labarun Hausa” suka wallafa.

(1) – Fati Washa: Jarumar ta dade ana damawa da ita a harkar fim din tun tana bayyana a matsayin ‘yar rawa har ta fara fitowa a tauraruwa a manyan fina-finai.

Sai dai an kula da yadda launin fatar ta ya sauya bayan ta samu karbuwa a harkar.

(2) – Sadiya Kabala: Da forko ta fara bayyana a fina-finai sai dai ta dena kasancewar tafi mayar da hankali akan sana’arta ta siya da sutturu.

Amma ga wadanda suka santa zasu kula da cewa launin fatarta ya sauya gaba daya.

(3) – Mansura Isah: Mansurah tsohuwar jarumar Kannywood ce kuma furodusa a halin yanzu, ita ce tsohuwar matar Sani Danja wanda ake zargin a masana’antar suka rabu, ita ma kwanan nan launin fatarta ya fara sauyawa.

(4) – Halima Atete: Ita ma ta dade tana cin zamaninta a masana’antar kasancewar ta iya hawa kowanne matsayi idan aka sanya ta, sai dai jama’a sun kula da yadda a hankali launin fatarta ya dinga sauyawa akan tsofaffin fina-finan ta.

(5) – Fati KK: Fati KK tsohuwar jarumar Kannywood ce wacce ta taka rawa sosai a fina-finan da ake yayi shekaru kusan goma da suka gabata kamar irin su, Ban Sake ta ba, Mijina ne da sauransu, bayan mutuwar auren ta ne ta dawo masana’antar da farar fata.

(6) – Maryam AB Yola: Maryam AB Yola tsohuwar jaruma ce wacce ta fara fitowa a shirin Adam Zango mai suna Nass, wanda daga bisani jarumin ya aureta.

Sai dai bayan auren nasu ya mutu ne ta dawo masana’antar da farar fata wacce harta kai ga wasu basu gane ta ba, ya fito ashirin Hafiz, daga bisani ta fita gaba daya daga masana’antar.

(7) – Sadiya Haruna: Sadiya Haruna ma tsohuwar jaruma ce wacce ta samu matsaloli kwarai da wasu manya a masana’antar kamar Alhassaan Kwalle, Teema Makamashi, Isah A Isah da sauransu, ita ma launin ta ya sauya kwarai.

(8) – Umma Shehu: Umma Shehu ma tsohuwar jaruma ce duk da dai dama tana da hasken fata amma ta kara musamman idan aka ga yadda ta sauya a cikin shirin Gidan Badamasi.