Ka bar ni in mori aure na: Uba ya koka kan yadda dansa ya ki barinsa da matarsa su kadaice

  • Wani dan Najeriya ya koka akan yadda dansa ya takura masa inda ya hana sa morar aurensa
  • A cewar mutumin, dansa yana makale wa matarsa don ba ya barinsu su kebe a matsayin ma’aurata
  • Matashin ya wallafa bidiyo inda yake tabbatar wa mutane yayin da aka dinga jajanta masa akan takurar da yaron ya yi musu

Wani mutum dan Najeriya ya wallafa bidiyon dansa mai suna Orji, wanda ya takura musu tare da hana su kebewa da mahaifiyarsa a matsayin ma’aurata, Legit.ng ta ruwaito.

Bayan wallafa kalubalen da ya ke fuskanta a TikTok, ya bayyana cewa tun bayan haihuwar yaron, ba sa morar aurensu a matsayin masoya da matarsa.

Don tabbatar wa da jama’a labarin, ya wallafa bidiyonsa tare da yaron a makale da matarsa wanda duk magiyar da su ka yi ya ki barinta.

Mahaifin mai suna Orij4dad a TikTok ya ce:

“Jama’a ban san me ke faruwa ba, ko dai duk masu aure ne ke fuskantar wannan kalubalen da zarar sun haihu? Tun bayan mun haifi yaron nan, duk sanda nake son kadaicewa da mata ta sai ya bi ta.”