Kalli video Yadda wakar “Warr” tasa aka binciko dukan da akayiwa Ado Gwanja tun 2017

Shahararren mawakin Hausa a arewacin Najeriya Ado Isah Gwanja yasaki wata sabuwar wakarsa maisuna “warr” wacce tana daya daga cikin wakar Hausa data samu karbuwa cikin kankanin lokaci.

Saidai tun bayan sakar wakar tasa irin kalaman da mawakin yayi nacewa “kafin asansu sunci kashin ubansu” hakan yasa aka lalubo wani tsohon hoton Ado Gwanja wanda akwai kulu a fuskarsa inda masoyansa a dandalin Facebook suke tambaya kodai wannan dukanma anyi masane kafin duniya tasansa.

Wannan kalaman na Ado Gwanja ba karyaba domin kuwa akwai manyan jaruman masana’antar Kannywood dasukasha wahala kafin sukai irin wannan matsayin dasuke dashi a halin yanzu irinsu Ali Nuhu, Adam a zango dadai sauransu.

Haka zalika wannan hoton a Ado Gwanja da aka dakesa a fuskarsa munsamu cikakken labarin daga shafin “Zuma Hausa times” inda sun wallafa labarin tun a wancan shekarar da abun ya faru.

Gadai cikakken abinda ya faru domin ku karanta