Karfin hali: Dan sanda Ya Kashe Wasu ‘Yan Bindiga 2 da Suka Kai Hari Gidansa

Labarai

Wani sufeton ‘yan sanda da ba a bayyana sunansa ba ya harbe wasu ‘yan bindiga biyu a unguwar Orogwe da ke karamar hukumar Owerri ta Yamma a jihar Imo.

Al’ummar Orogwe ita ce wurin da wasu ‘yan bindiga suka kai farmaki kwanan nan suka kashe mutane bakwai Hukumomin ‘yan sanda a Imo sun tabbatar wa mazauna garin cewa ‘yan sandan sun dukufa wajen kamo masu laifin tare da tabbatar da tsaron jihar.

An kashe wasu ‘yan bindiga biyu a ranar Alhamis yayin da suka kai hari a gidan wani sufeton ‘yan sanda a garin Orogwe garin da ke a karamar hukumar Owerri ta Imo state.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Michael Abattam ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, amma bai bayyana sunan sufeton ‘yan sandan ba,

Ya ce ‘yan bindigar sun tsallake shingen gidansa ne kana suka shiga harabar gidan inda suka lalata masa kofa, amma sufeton ‘yan sandan ya yi dauki ba dadi dasu.

News All.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *