Kaso 70 na mata na yin bidiyon tsiraicinsu su adana a wayoyinsu inji Safara’u

Fitacciyar mawakiya kuma tsohuwar jarumar cikin shirin Kwana casa’in Safiyya Yusuf da aka fi sani da Safara’u ta ce kaso saba’in cikin dari na mata suna daukar bidiyon tsiraicinsu su aje a wayarsu ta hannu ba ita kadai ba natan ne dai ya fito fili.

 

Jarumar ta bayyani hakan ne a yayin wata hira ta musamman da sashen Hausa na BBC ya yi da ita kuma shafin mu na labarai.com.ng ya kalli hirar.

Safara’u ta ce ta shafe akalla kusan watanni 3 kacal tana jimami bayan Bullard bidiyon nata amma daga baya iyayenta suka kwantar mata da hankalinta kan cewa kaddara hakan zai iya faruwa a kan kowa.