Wani dalibi dan aji 3 a fannin lissafi a Jami’ar Bayero ta Kano ya koka kan yadda shaidarsa ta makaranta zata daina amfani, kuma bai kammala karatun nasa ba.
A wata tattaunawa da aka yi da dalibin ya bayyana yadda ya fara sana’a a shekarar 2020, kuma yake fatan karfafa ta a yanzu.
Dalibai da dama a Najeriya sun kama sabbin sana’o’i sakamakon jarrabawar da ASUU ta jefa su na zaman gida, kamar yadda shafin “Hausa.Legit.ng” suka kawo cikekken rahoton.
Abdulhadi Dan kama ya samu shiga
sashen ilmin lissafi a jami’ar Bayero ta jihar Kano domin yin digirinsa na farko, ya kamata Dan kama ya kammala digirinsa a yanzu idan da yajin aikin da kungiyar malaman jamio’i ta fara ba kan rashin jituwa da gwamnatin tarayya bata shafe shi ba.
Zaku yi tunanin Dan kama wanda a yanzu yana aji 3 zai kosa ya koma makaranta domin ya gaggauta kammala karatunsa.
Sai dai ga dukkan alamu tunanin matashin ya kau ya bar batun neman digirin da yake yi tun da yace, bai damu ba ko da ASUU sun ki amincewa a bude jami’o’i.
A farkon barkewar cutar ta Korona a shekrara 2020, Dan kama ya fara kasuwancin siyar da ‘yayan itace, ya fara tane ta wata hanya ta musamman domin kuwa shi har ta yanar gizo yana iya siyarda hajarsa.
Lokacin da batun Korona ya lafa, kuma aka koma makaranta Dan kama bai daina siyar da yayan itace ba, Maimakon haka ya kafa kasuwa mai karfi.
Dan Kama ya tuna yadda ya fara: Na fara siyar da ‘yayan itatuwa a lokacin kulle-
kulle Korona, a cikin watan Ramadan mutane suna gida sabida cutar basa zuwa ko’ina don haka lokacin ne tunanin yazo min.
Nayi tunanin tun watan Ramadana ne kuma mutane suna bukatar ‘yayan itatuwa, me zai hana in gwada siyarwa ta yanar gizo?.
Yace, kasuwancin ‘yayan itacen da ya fara ta yanar gizo ya bunkasa a lokacin barkewar cutar tun a lokacin yakan kai wa abokan cinikinsa hajarsa har gida kyauta.
Kana ya kara da cewa: Na fara ta yanar gizo ne sabida ban taba ganin wanda ya gwada hakan ba, yawancin abokaina basu yarda da tunanin kasuwancin ba amma duk da haka na je na fara, suna kallon kasuwancin a matsayin karami.
Babu shakka lokacin da Legit.ng ta zanta da Dan kama, batutuwansa sun tabbata irin kaunar da yake wa sana’ar tasa daya fara, yana matukar son kasuwancin ‘yayan itatuwa kuma yana shirin fadada jari.
Ba don yajin aikin ASUU ba, ta tuni ya kammala ya fice daga jami’ar Bayero ya maida hankali kan harkokinsa na sana’a kamar yadda yace, yana shirin bude sabbin rassa a jihar.
Hakan bai samu ba kasancewar ASUU ta fara yajin aiki, lamarin da ya shafi dalibai da dama ciki har da Dan kama.
Amma da alama Dan kama bai damu da abin dake faruwa na yaji ba domin ya shaida wa Legit.ng cewa, ya kamata ma a cigaba da yajin aikin domin ya samu ya kammala shirya kasuwancinsa.
Leave a Reply