Kotu Ta Umarci Wani Ma’akacin Gwamnati Ya Dawo Da Albashinsa Na Shekara Goma Sha Daya

Abun mamaki baya karewa a wannan rayuwa inda wata babban kotu a jihar Filato ta umarci wani babban ma’aikacin cibiyar nazarin lafiyar dabbobi ta kasa (NVRI) da ke Vom a jihar Filato, Muhammed Nasiru, da ya amayo albashin shekara 11 da ya amsa a matsayin babban jami’in sashin mulki na NVRI.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Christy Dabup, ya samu Nasiru ne da laifin da ake zarginsa tare da yanke masa hukuncin zaman gidan yari na wata bakwai ko zabin biyan tara na N150,000.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ce ta gurfanar da Nasiru a gaban kotun bisa tuhume-tuhume guda biyu da suka hada da bayyar da takardun karya da kasa iya gabatar da sahihin takardun neman aiki da cibiyar nazarin lafiyar dabbobi ta NVRI.

ICPC ta ce Nasiru bai cancanci samun damar daukar aiki ba bisa dalilin cewa an taba masa ritayar dole a cibiyar kula da harkokin shari’a ta kasa da ke Abuja (NJI) a shekarar 2003.

Bayan da kotun ta kama wanda ake zargin da aikata manyan laifuka, ta umurce shi da ya dawo da albashin shekara 11 da ya karba wa hwamnatin tarayya kuma zai shafe watanni bakwai a daure.

Alkalin kotun da yake yanke hukunci, ya ce Lauyan ICPC, Evans Peter, ya iya gamsar da kotun kan zarge-zargen da suke yi ma wanda suke kara, a yayin da kokarin kariya na Muhammed Nasiru suka gaza kare kansu.