Kotu ta yanke hukuncin kisa kan wanda ake zargi da kashe Hanifa Abubakar

Wata babbar kotu a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta yanke hukuncin kisa kan Abdulmalik Tanko kan samun sa da laifin kashe dalibarsa Hanifa Abubakar.

Mai Shari’a Usman Na’abba da ke jagorantar ƙarar ne ya yanke hukuncin a ranar Alhamis 28 ga watan Yulin 2022.

Ana zargin malaminta Abdulmalik Tanko ne ya sace ta a watan Disambar 2021 tare da kashe yarinyar mai shekara biyar, kana ya binne gawarta a gidansa.

Kotun ta sami Abdulmalik Tanko da laifin garkuwa da Haneefa, da laifin kisanta da kuma laifin kitsa yadda za a yi garkuwa da ita.

Sannan kotu ta sami Hashimu Isyaku da laifin hada kai wajen kisan Hanifa da ɓoye laifin aikata garkuwa da Hanifa, sannan yana da masaniya an yi garkuwa da Hanifar.

Sannan kotu ta wanke Fatima Jibril daga zargin rubuta wa iyayen Hanifa wasikar sanar da su an yi garkuwa da ita.

Sai dai ta same ta da laifin hannu waje yin garkuwa da Hanifa, da masaniyar an yi garkuwa da ita.

Hukuncin da aka yanke

Bayan karanto laifukan da aka tabbatar wa waɗanda ake tuhumar, dukkan su sun nemi kotun da ta yi musu sassauci.

Kotu ta yanke wa Abdulmalik hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin garkuwa da Hanifa da ɗaurin shekaru biyar a gidan gyaran hali na garkuwa da mutum.

Kotu ta yanke wa Fatima hukuncin shekara biyu a gidan gyaran hali kasancewarta uwa.

Ta kuma yanke wa Hashimu hukuncin ɗaurin shekara biyu a gidan gyaran hali sannan daga baya a kashe shi.

An fara zaman kotun na yanke hukunci a karkashin Mai Shari’a Usman Na’abba.

Tuni aka gabatar da wadanda ake zargi su uku a gaban kotun.

Barista Musa Lawan, Kwamishinan Shari’a na Kano, shi ne ke jagorar lauyoyin gwamnati.

Ita kuma Barista Asiya Mohammad tana jagorantar lauyoyin da ke kare Abdulmalik Tanko da sauran mutum biyu da ake zargi da hannu a kisan Hanifa Abubakar.