KWAMANDAN ’YAN FASHIN DAJI ZAI AURI DAYA DAGA CIKIN FASINJAN JIRGIN KASAN ABUJA ZUWA KADUNA.

Kwamandan ’yan ta’adda da suka sace fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna na shirin auren wata budurwa daga cikin fasinjojin.

Dan jarida Tukur Mamu, wanda ke shiga tsakani ya kuma taimaka aka sako wasu daga cikin fasinjojin, shi ne ya koka kan shirin kwamandan ’yan ta’addan na auren Azurfa Lois John mai shekara 21.

Tukur Mamu ya ce wata majiya mai tushe ta shaida masa cewa idan ba a dauki matakin gaggawa ba ’yan ta’addan za su aurar da budurwar nan ba da dadewa ba.

Mawallafin jiardar Desert Herald ya yi kira ga Gwamantin Tarayya da Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) su gaggauta yin abin da ya dace don kubutar da budurwar domin kada a maimaita abin da ya faru da Leah Sharibu.

Wani kwamandansu ’yan ta’addan yana son ta, don haka ya kamata a kula da dauki matakin da ya dace cikin gaggawa.

“Duk da cewa na san wannan bayani zai kawo damuwa ga ’yan uwanta da ’yan Najeriya baki daya, yin hakan ya zama wajibi don gudun kada a maimaita irin na Leah Sharibu.

“Ina rokon kungiyar CAN musamman da kada ta siyasantar da wannan batu ko dauke shi a matsayin sanarwa kawai kamar yadda na gani a baya.

“Ta hanzarta hada kai da hukumomin da suka dace domin tunkarar wadanda suka sace budurwar kafin lokaci ya kure.

“A yayin da wannan lamarin ke kara ta’azzara, ina rokon Gwamnati Tarayya ta yi gaggawar ganin an sako sauran fasinjojin da aka sace su tare,” inji sanarwar da Tukuar Mamu ya fitar.