Kwamcala – Ƙabilar Da Uwar Amarya Ke Kwana Da Ango Domin Tabbatar Da Ƙwazonsa

A mafi yawan ƙabilun nahiyar Afrika, ana ɗora wa kan mahaifiya alhakin faɗakar wa da yin nasiha ga budurwar da za a aurar.

A mafi yawancin lokuta, ƙanwar mahaifiya ce ke shirya budurwa domin ta fuskanci ƙalubalen da ke cikin zaman aure.

Amma lamarin ba haka ya ke ba a ƙabilar Banyankole da ke Kudu maso Yammacin ƙasar Uganda, inda aka ɗora wa ƙanwar mahaifiyar budurwar da za a aurar alhakin sanin namijin da za a bawa auren ɗiyar ƴar uwar ta.

Babban aikin ƙanwar uwar budurwar da za a aurar a ƙabilar Banyankole shine tabbatar da kuzarin ango ta fuskar saduwa kafin a kai ga aura masa ɗiyar ƴar uwar ta.

Domin tabbatar da kuzarin angon, a wasu lokutan, ƙanwar mahaifiyar kan yi saduwar jima’i da angon ɗiyar ƴar uwarta domin tabbatar da ƙwazonsa a gado.

Kazalika, ƙanwar mahaifiyar budurwar za ta bawa angon tabbacin cewa ɗiyarsu cikakkiyar budurwa ce da ba ta taɓa sanin wani ɗa namiji ba.

Ita ce kuma ke da alhakin tabbatar da cewa diyarsu da zasu aurar ba ta taba sanin wani ɗa namiji ba ta hanyar duba tsiraicinta da yi mata binciken ƙwaƙwaf kafin aurar da ita ga saurayin da ke son aurenta.

A wasu lokutan, ƙanwar mahaifiyar kan kwana tare da ma’auratan a daren farko na aurensu domin ji da ganin yadda zasu ci amarci, saboda kawai ta tabbatar da kuzarin angon da suka aura wa ɗiyarsu.

Duk da ana yi wa wannan al’ada kallon tsohon yayi, ta nuna yadda ƙabilar Banyankole, musamman masu yaren Bahima, suka bawa rike budurci muhimmanci.

Da zarar ɗiyar ƴan ƙabilar Bayankole ta cika shekaru 8 a duniya, za a fara saka mata matakai da takunkumi daban-daban domin fara yi mata shirin aure.

Duk da ƴan ƙabilar Bayankole kan gudanar da al’adu dadan-daban yayin auren ƴaƴansu, al’adar tabbatar da ƙwazon ango da budurcin amarya da ƙanwar mahaifiyar budurwa ke yi kafin kulla aure ta fi zama babban abun mamaki.

Kuci gaba da kasancewa tare da News All don samun sabbin labarai.