Kwararriya dalibar mathematics yar shekara 14 daga arewacin Nigeria ta cinye gasar math ta duniya

Fatima Adamu Maikusa, kwararriy a fannin ilmin lissafi ‘yar Najeriya, ‘yar shekaru 14, ta kafa tarihi mai ban mamaki, bayan da ta samu lambar yabo 7 a fagen gasar Math ta duniya.

Fatima Adamu, wacce a halin yanzu daliba ce a makarantar Nigerian Turkish International School (NTIC), Kano, Nigeria, ‘yar asalin garin Gombe ce a Arewacin Najeriya.

Dangane da bayanin da makarantarta ta bayar Fatima ta fara karatun lissafi tun tana da shekaru 9.

Daga nan ta ci gaba da cin nasara kamar gasar Lissafi ta Duniya a Jakarta, Indonesiya, da Gasar Lissafin Amurka (AMC 08).

Ta kuma ci nasarar kalubalan lissafi na kasa da kasa a Bangkok Thailand, da Kangourou sans frontiers -KSF lissafi gasa, Future Intelligence Students olympiad (FISO), Lissafi ba tare da iyaka ba a Bulgaria da kuma Komodo math a Indonesia.