Kyautar Da Atiku ya yiwa Naziru Sarkin waka Ta girgiza kannywood
Dan takarar shugaban kasa Na jam’iyyar PDP mai suna Atiku Abubakar ya yiwa mawaki naziru Sarkin waka wata kyauta wacce ta kayatar dashi kuma ta kara masa girma a idon duniya da kuma jama’a
Idan baku mantaba a kwanakin baya ne dai naziru yayiwa Atiku wata sabuwar waka ta kamfen da kuma cin mutuncin ga jami’ya mai mulki wanda hakan ya faranta ran Atiku kuma yaji dadi sosai
Da farko dai mutane harsun fara surutai akan cewa yayi waka amma kuma ba’a bashi komai wanda hakan yasa kamar kwarin gwiwar atikun ya rago wai yasan bafa lallai yaci zabe ba cewar magoya bayan shugaba buhari.
Sai gashi daga bisani ya bawa mutane mamaki wanda ya baiwa mawakin kyautar dankareriyar mota da kuma makudan kudade wanda a yanzu babu wani mawaki ko dan film da aka taba yiwa wannan kyautar hakan ya bawa yan kamnywood mamaki matuka da gaske
Wanda har wasu sun fara guna gunin cewa ai daman naziru ya kware wajen maula a waka wanda wasu ke ganin kamar hassada ce kawai da ake yiwa wannan mawakin mudai babu abinda zamu ce sai dai Allah ya sanya alkhairi ya kuma kara basira Sarkin waka

Leave a Reply