macijine shi page 13 – 14

🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄

MACIJINE🪱🪱🪱

Na mammy kabeer
(Anty mammy)

Elegant online writers📚📚

Free book

Page 13/14

________“Wayyo Allah na Mai taimako kana ina?kazo gareni,ina buƙatar tallafinka,ahhhhhhhhh !!!fattu ta kwalla ƙara mai tsananin ƙarfi lokacin da taji hannun maigari na ƙoƙarin taɓa mata dukiyar fulani tana mai buge hannunsa daga kan ƙirjinta.

Ɗaga hannu maigari yayi cikin fushi ya sake ɗauke fattu da wani gigitaccen mari,dan ya fuskanci tana ƙoƙarin kawo masa cikas akan ƙudurinsa,shikuwa ya rantse yau bazai bar wannan damar ta wuce shi ba.
“Dan ubanki ki tsaya nayi- nayi abinda ke gabana,wllh yau ko ubankine bukar zai zo gurin nan bai isa ya hanani aiwatar da ƙudirina akanki ba”mai gari ya faɗa yana ƙara ƙoƙarin maida hannunsa gurin dake tsole masa idanu,wato breast ɗin fattu.

Saidai kafin hannunsa ya sauƙa ga inda yayi nufin ,yaji wata irin shaƙa da tunda yake arayuwarsa bai taɓa tsintar kansa cikin irin makamancin wannan shaƙar a aduniya ba.
Ta ko ina yaji shi aɗaure dam-dam kamar ƙullin buhun goro.

Cikin azaba da fizgar magana mai gari yace “wayyo Allah hannuna,na shiga uku wayyo zan mutu” ya faɗa idanunsa azazzare kamar zasu fito tsabar azaba.

Cikin hanzari fattu wacce idanunta ke rufe, ta riga ta gama fitar da rai ta sadaƙar cewa yau shikenan ta rasa budurcinta ,dan ta san ba mai zuwa ya ceceta ,koda tayi ihu ba mai jin sautin ihunta,sakamakon ruwan saman da ake tsugawa.ba zato ba tsammani tajiyo ihun maigari lokacin da maciji yayi sama dashi ya cilla shi can gefe guda ,bayan tabbatar da cewa mai gari ya suma.ji kake ƙasss-ƙasss,hannu da ƙafar mai gari na bangaren dama sun karye.

Da sauri fattu ta kalli inda akayo jifa da mai gari dan tabbatar da cewar shiɗin ne kokuma yaya.aikuwa cikin wani irin farin ciki da murna ta yunƙura da ƙyar ta zauna tana kuka da dariya,sai kuma ta tafi gareshi cikin rarrafe tana zuwa inda macijin ke tsaye yana huci ya ƙure mai gari da ido,da alama yana son ganin maigari ko zaiyi wani motsin