
MANUFAR KAFA KUNGIYAR #IZALA A NIJERIA DA SAURAN KASASHE!!!
Rubutawar Ibrahim Baba Suleiman âď¸
JIBWIS Kungiyar kawar da Bidiâah ta tsai da Sunnah.
Wannan qungiya ta alâummar musulmi an kafa ta ne tun a shekarar 1978 a Najeriya, kuma shugabanta na farko shi ne Alhaji Musa Maigandu Muhammad, a qarqashin kulawar Malam Abubakar Mahmud Gumi, tare da Sheikh Ismaâil Idris bn Zakariyya, a matsayin shugaban majalisar malamai na farko na kungiyar.
Wannan Kungiya ta musulunci ce, wacce musulmi suka kafa mai helkwata a Jos, Jihar filato, wanda yanzu Helkwatar ke birnin tarayya Abuja. inda anan ne ofishin Shugaban ta na kasa yake a halin yanzu, kungiyar bata da alaka ko wace iri ce, da wata kungiyar asiri, darika ko kuma kungiyar Siyasa.
Wannan kungiya tana kan tafarkin musulunci ne wanda ta dogara ga Qurâani da hadisan Annabi Muhammad (SAW) Bisa fassarar Magabata. Babu bambanci a cikin kungiya in dai har mutum musulmi
ne da yayi Imani da âAllahâ kamar yadda Annabi Muhammad (SAW) ya karantar. Kungiya na maraba da irin wannan mutum da kuma shawarwarinsa masu amfani wadanda suka dace da musulunci.
Qungiyar ita ce irinta ta farko a tarihin yada addinin musulunci a Najeriya, hadi da harkar ilmantarwa, tare da daukaka darajar harkokin addinin Musulunci ba tare da wani tsoro ba. Don haka ne sai kungiyar ta sanya wasu ginshiqan #MANUFOFI da take so ta cimma domin kai wa Ga gaci.
Daga cikin muhimman manufofin wannan kungiya sun hada da:
– Kawar da duhun jahilci daga cikin alâumma, wanda ya yi wa alâumma katutu.
– Hada kan alâummar musulmi a bisa koyarwar Alqurâani da Sunnar Manzon Allah (SAW),
– Wayar da kan alâummar musulmi game da alâamuran addini, domin a gudu tare a tsira tare.
– Fadakar da alâummar musulmi domin a yi watsi da wasu miyagun littattafai da suke tura mutane cikin halaka.
– Tabbatarwa da cewa Annabi (SAW) ya kammala isar da sakon Allah (SWT).
– Duk wanda ya yi daâawar annabta, ko kuma yake riya cewa Annabi (SAW) yana ziyartarsa da wani sako, to wannan zunzurutun makaryaci ne.
– Yada Musulunci a Najeriya da wajen Najeriya.
– Yin daâawa a kan fadin Manzon Allah (SAW) cewa: âduk wanda ya ga abin qi, to ya sauya shi da hannunsa, idan ba zai iya ba, to da harshensa, in ba zai iya ba, to da zuciyarsa, amma wannan shi ne mafi raunin imani.â
– Kar a boye hujja in dai har ta tabbata daga littafin Allah Madaukakin Sarki, ko sunnar Manzon Allah (SAW).
Wasu daga cikin ayyukan kungiyar sun Hada da:
Kasancewar wannan kungiya ta shahara sosai a kasashe daban-daban na duniya, wannan ya sa aka samar da kwamitoci daban-daban domin gabatar da ayyuka da yawa. Kadan daga cikin kwamitocin kungiyar tare da wadanda suke jagorantar kwamitocin, sun hada da:
– Kwamitin Daâawah:
Karkashin Sheikh Yakubu Musa Hassan.
– Kwamitin Sulhu da fatawa
Karkashin Sheikh Usman Isa Taliyawa Gombe
– Kwamitin ladabtarwa da walwala.
Karkashin Sheikh Habibu yahaya kaura
– Kwamitin Fatun Layya.
Karkashin Sheikh Habibu Yahaya Kaura
– Kwamitin Taimakon Gaggawa.
Karkashin Sheikh Habibu Yahaya Kaura
– Kwamitin Ayyuka.
Karkashin Sheikh Abubakar Giro Argungu.
– Kwamitin Kula da Marayu
Karkashin Ambasada Garba Aminci.
– Kwamitin Ilimi.
Karkashin Sheikh Prof. Abdullahi Saleh Pakistan
-Kwamitin MANARA TV.
-kwamitin yada labarai
Karkashin kulawar shugaban riko, Nasiru Adamu El-hikaya.
-Kwamitin yanar Gizo.
Karkashin Alhaji Ibrahim Baba Suleiman
Da Sauran wasu kwamitoci.
Shugaban kungiyar IZALA na Naijeriya a wannan lokaci shi ne Ash-Sheikh Imam (Dr.) Abdullahi Bala Lau, khalifa na farko a sashin Shugabancin kungiyar tun bayan kafa ta, wanda shi Ne tsohon mataimakin shugaban kungiyar bayan rasuwar Marigayi Sheikh Imam Ikara, duk a zamanin shugabancin marigayi Alh. Musa maigandu Muhammad.
Sheikh Abdullahi Bala Lau ya gaji shugabancin kungiyar ne bayan rasuwar Shugaban IZALA na farko Sheikh Musa Maigandu Muhammad.
Kazalika akwai masu rufa masa baya a fagen shugabanci irin Su:
– Sheikh Usman Isah Taliyawa Gombe: Mataimakin Shugaban Kungiya Na kasa na daya.
-Sheikh Abbas Muhammad Jega: Mataimakin Shugaban Kungiya na kasa na biyu.
– Sheik Dr. Ibrahim Jalo Jalingo: Shugaban Majalisar Malamai na kasa.
– Sheik Barrister Ibrahim Sabi’u Jibia: Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai na Kasa.
– Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe: Babban Magatakardan kungiyar na kasa.
– Engineer Mustapha Imam Sitti: Daraktan Rundunar ‘Yan Agaji na Kasa
– Alhaji Muhammad Kabir Sa’id Gusau: Mataimakin Daraktan Agaji na kasa (Deputy Director Training & operation)
-Alhaji Abdullahi A. Diggi: Mataimakin Daraktan Agaji na kasa (Deputy Director Training & Finance)
-Ustaz Aliyu Abubakar Dan Agaji Jega
Mataimakin darakta na biyu, (Assistant Director Admin and Finance)
-Muhammad Sani Mina
Mataimakin darakta na biyu, (Assistant Director Training and operation)
Kungiayar IZALA ta sake garambawul wajen kirkirar kwamitoci domin ayyukan wa’azi ya tafi cikin tsari kuma a zamanace.
Gasu kamar haka:
kungiyar ta samu karbuwa a sassa daban-daban na duniya. A Najeriya tana da rassa a dukkanin jihohin Najeriya 36 da birnin tarayya Abuja. Haka kuma saboda irin yadda kungiyar take kokarin ilmantar da alâumma, wannan ya sa har ta sami kutsawa zuwa ga wasu kasashe, kamar su; Kasar Saudi Arabia, Amurka, Burtaniya, da sauran kasashen turai, da kuma kasashen afurka irin su Nijer, kotonu, Mali, Senegal, Togo, Kamaru, Chadi, Burkina faso, Gini, da da sauransu.
Wasu daga cikin abubuwan da kungiyar ta mayar da hankali wajen yin su, sun hada da:
– Koyarwa a bisa tafarkin Manzon Allah (SAW) ba tare da bin son zuciya ko kuma yin makauniyar biyayya ga wani ba.
– Tsantsar karantar da hakikanin ilimin addinin Musulunci.
– Gabatar da waâazin kasa a duk makwanni Uku ko hudu ko adadin wasu kwanaki da akayi matsaya a kai don tunatar da mutane abin da suka manta daga littafin Allah da manzon sa SAW.
– Kafa makarantu domin koyar da ilimin addini da na boko, da sauran fannonin ilimi.
– Kai Ziyara Zuwa gidajen marayu, fursina da asibitoci, domin tallafawa musulmai marasa galihu.
– Samar da taimakon gaggawa a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
kungiyar ta samar da hamshaqan malamai a sassa wadanda suka sami daukaka ta ilimi a fadin duniya baki daya, saboda jajircewa da kokarin bin tafarkin Manzon tsira, Annabi Muhammad (SAW), sau da kafa.
Dan haka nema kungiyar take rubuta “LAA ĆAA’ATA LIMAKHLUĆIN FII MA’ASIYATIL KHALIĆI.” A dukkan kadarorinta data Mallaka, irin su motoci da sauran su, Tun farkon kafa kungiyar har zuwa yau dinnan kungiyar bata chanza ba.
Haka kuma ta ko wacce fuska tarihin izala zaizo dogo ko gajere, ba za a taba mantawa da irin gudummar da marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ya bada ba wajen kafa wannan kungiya mai tarin albarka ba.
Hakazalika Tarihin IZALA bazai kammala ba tare da an ambaci Marigayi Sheikh Isma’ila Idris Ibn Zakariyya (Shugaban Majalisar Malamai na farko) da irin gudunmawar da ya bayar dan kafuwar wannan kungiya mai albarka, da irin Su Marigayi Sheikh Ibrahim Bawa Maishinkafa, Marigayi Sheikh Hudu Chikaji Zariya, Marigayi Sheikh Adam Mai Shafi, Marigayi Sheikh Abubakar Imam Ikara, Marigayi Sheikh Musa Maigandu Muhammad, Marigayi Alhaji Ali Ibrahim Tofa (Tsohon Shugaban yan agaji na kasa), Marigayi Sheikh Rabi’u Aliyu Daura, Marigayi Sheikh Dr. Alhassan Sa’id Adam Jos, marigayi Sheikh Adamu Aliyu maigora, marigayi Sheikh Rabi’u Aliyu Daura, marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam koda Kuwa ba manufarmu mu zayyana sunan kowa ba.
Suma sauran Matasan Malaman da a baya suka bada Gudunmawar su dan kungiyar ta cimma manufofinta, wanda a yanzu sun zama Dattawa, a farkon tafiya gashin su baki ne, amma yanzu ya rikide ya zama fari sol, kuma ba’a daina yin wa’azin ba, irin su Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina, (Trustee) na kungiyar, wanda a farkon tafiya shine Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai na biyu, Sheikh Usman Isah Taliyawa Gombe, Sheikh Abbas Muhammad Jega, Alaramma Abubakar Adam Katsina da Sheikh Habibu Yahaya Kaura wanda ake masa lakabi da dan autan masu wa’azi, sabo da kankantar sa, gashi yanzu shekaru sun cimmasa, da sauran wadanda suke raye ake fafatawa da su a halin yanzu irin su Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe, Sheikh Abubakar Giro Argungu, da dai sauransu.
Daga karshe Muna addu’a ga dukkan wadanda suka sadaukar da dukiyoyin su da kuma rayukansu akan wannan harka taci gaban addini, Allah ya saka musu da gidan Aljanna ya hada mu dasu a babban matsayi a lahira. Amin.
jibwisnigerian@gmail.com
WANNAN SAKO NE DAGA KWAMITIN YANAR GIZO TA KUNGIYAR IZALA TA KASA, (JIBWIS SOCIAL MEDIA).
JIBWIS NIGERIA đłđŹ
CC:
Abdullahi Bala Lau
Muhammad Kabir Haruna
Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Nigeria
MANUFAR KAFA KUNGIYAR #IZALA A NIJERIA DA SAURAN KASASHE!!!Rubutawar Ibrahim Baba Suleiman âď¸JIBWIS Kungiyar kawar da Bidiâah ta tsai da Sunnah.Wannan qungiya ta alâummar musulmi an kafa ta ne tun a shekarar 1978 a Najeriya, kuma shugabanta na farko shi ne Alhaji Musa Maigandu Muhammad, a qarqashin kulawar Malam Abubakar Mahmud Gumi, tare da Sheikh Ismaâil Idris bn Zakariyya, a matsayin shugaban majalisar malamai na farko na kungiyar.Wannan Kungiya ta musulunci ce, wacce musulmi suka kafa mai helkwata a Jos, Jihar filato, wanda yanzu Helkwatar ke birnin tarayya Abuja. inda anan ne ofishin Shugaban ta na kasa yake a halin yanzu, kungiyar bata da alaka ko wace iri ce, da wata kungiyar asiri, darika ko kuma kungiyar Siyasa.Wannan kungiya tana kan tafarkin musulunci ne wanda ta dogara ga Qurâani da hadisan Annabi Muhammad (SAW) Bisa fassarar Magabata. Babu bambanci a cikin kungiya in dai har mutum musulmi ne da yayi Imani da âAllahâ kamar yadda Annabi Muhammad (SAW) ya karantar. Kungiya na maraba da irin wannan mutum da kuma shawarwarinsa masu amfani wadanda suka dace da musulunci. Qungiyar ita ce irinta ta farko a tarihin yada addinin musulunci a Najeriya, hadi da harkar ilmantarwa, tare da daukaka darajar harkokin addinin Musulunci ba tare da wani tsoro ba. Don haka ne sai kungiyar ta sanya wasu ginshiqan #MANUFOFI da take so ta cimma domin kai wa Ga gaci.Daga cikin muhimman manufofin wannan kungiya sun hada da:- Kawar da duhun jahilci daga cikin alâumma, wanda ya yi wa alâumma katutu.- Hada kan alâummar musulmi a bisa koyarwar Alqurâani da Sunnar Manzon Allah (SAW),- Wayar da kan alâummar musulmi game da alâamuran addini, domin a gudu tare a tsira tare.- Fadakar da alâummar musulmi domin a yi watsi da wasu miyagun littattafai da suke tura mutane cikin halaka.- Tabbatarwa da cewa Annabi (SAW) ya kammala isar da sakon Allah (SWT).- Duk wanda ya yi daâawar annabta, ko kuma yake riya cewa Annabi (SAW) yana ziyartarsa da wani sako, to wannan zunzurutun makaryaci ne.- Yada Musulunci a Najeriya da wajen Najeriya.- Yin daâawa a kan fadin Manzon Allah (SAW) cewa: âduk wanda ya ga abin qi, to ya sauya shi da hannunsa, idan ba zai iya ba, to da harshensa, in ba zai iya ba, to da zuciyarsa, amma wannan shi ne mafi raunin imani.â- Kar a boye hujja in dai har ta tabbata daga littafin Allah Madaukakin Sarki, ko sunnar Manzon Allah (SAW).Wasu daga cikin ayyukan kungiyar sun Hada da:Kasancewar wannan kungiya ta shahara sosai a kasashe daban-daban na duniya, wannan ya sa aka samar da kwamitoci daban-daban domin gabatar da ayyuka da yawa. Kadan daga cikin kwamitocin kungiyar tare da wadanda suke jagorantar kwamitocin, sun hada da:- Kwamitin Daâawah:Karkashin Sheikh Yakubu Musa Hassan.- Kwamitin Sulhu da fatawaKarkashin Sheikh Usman Isa Taliyawa Gombe- Kwamitin ladabtarwa da walwala. Karkashin Sheikh Habibu yahaya kaura- Kwamitin Fatun Layya.Karkashin Sheikh Habibu Yahaya Kaura- Kwamitin Taimakon Gaggawa.Karkashin Sheikh Habibu Yahaya Kaura- Kwamitin Ayyuka.Karkashin Sheikh Abubakar Giro Argungu.- Kwamitin Kula da MarayuKarkashin Ambasada Garba Aminci.- Kwamitin Ilimi.Karkashin Sheikh Prof. Abdullahi Saleh Pakistan-Kwamitin MANARA TV.-kwamitin yada labaraiKarkashin kulawar shugaban riko, Nasiru Adamu El-hikaya. -Kwamitin yanar Gizo.Karkashin Alhaji Ibrahim Baba SuleimanDa Sauran wasu kwamitoci.Shugaban kungiyar IZALA na Naijeriya a wannan lokaci shi ne Ash-Sheikh Imam (Dr.) Abdullahi Bala Lau, khalifa na farko a sashin Shugabancin kungiyar tun bayan kafa ta, wanda shi Ne tsohon mataimakin shugaban kungiyar bayan rasuwar Marigayi Sheikh Imam Ikara, duk a zamanin shugabancin marigayi Alh. Musa maigandu Muhammad.Sheikh Abdullahi Bala Lau ya gaji shugabancin kungiyar ne bayan rasuwar Shugaban IZALA na farko Sheikh Musa Maigandu Muhammad.Kazalika akwai masu rufa masa baya a fagen shugabanci irin Su:- Sheikh Usman Isah Taliyawa Gombe: Mataimakin Shugaban Kungiya Na kasa na daya.-Sheikh Abbas Muhammad Jega: Mataimakin Shugaban Kungiya na kasa na biyu.- Sheik Dr. Ibrahim Jalo Jalingo: Shugaban Majalisar Malamai na kasa.- Sheik Barrister Ibrahim Sabi’u Jibia: Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai na Kasa.- Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe: Babban Magatakardan kungiyar na kasa.- Engineer Mustapha Imam Sitti: Daraktan Rundunar ‘Yan Agaji na Kasa- Alhaji Muhammad Kabir Sa’id Gusau: Mataimakin Daraktan Agaji na kasa (Deputy Director Training & operation)-Alhaji Abdullahi A. Diggi: Mataimakin Daraktan Agaji na kasa (Deputy Director Training & Finance)-Ustaz Aliyu Abubakar Dan Agaji JegaMataimakin darakta na biyu, (Assistant Director Admin and Finance)-Muhammad Sani Mina Mataimakin darakta na biyu, (Assistant Director Training and operation)Kungiayar IZALA ta sake garambawul wajen kirkirar kwamitoci domin ayyukan wa’azi ya tafi cikin tsari kuma a zamanace.Gasu kamar haka:kungiyar ta samu karbuwa a sassa daban-daban na duniya. A Najeriya tana da rassa a dukkanin jihohin Najeriya 36 da birnin tarayya Abuja. Haka kuma saboda irin yadda kungiyar take kokarin ilmantar da alâumma, wannan ya sa har ta sami kutsawa zuwa ga wasu kasashe, kamar su; Kasar Saudi Arabia, Amurka, Burtaniya, da sauran kasashen turai, da kuma kasashen afurka irin su Nijer, kotonu, Mali, Senegal, Togo, Kamaru, Chadi, Burkina faso, Gini, da da sauransu.Wasu daga cikin abubuwan da kungiyar ta mayar da hankali wajen yin su, sun hada da:- Koyarwa a bisa tafarkin Manzon Allah (SAW) ba tare da bin son zuciya ko kuma yin makauniyar biyayya ga wani ba.- Tsantsar karantar da hakikanin ilimin addinin Musulunci.- Gabatar da waâazin kasa a duk makwanni Uku ko hudu ko adadin wasu kwanaki da akayi matsaya a kai don tunatar da mutane abin da suka manta daga littafin Allah da manzon sa SAW. – Kafa makarantu domin koyar da ilimin addini da na boko, da sauran fannonin ilimi.- Kai Ziyara Zuwa gidajen marayu, fursina da asibitoci, domin tallafawa musulmai marasa galihu.- Samar da taimakon gaggawa a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.kungiyar ta samar da hamshaqan malamai a sassa wadanda suka sami daukaka ta ilimi a fadin duniya baki daya, saboda jajircewa da kokarin bin tafarkin Manzon tsira, Annabi Muhammad (SAW), sau da kafa.Dan haka nema kungiyar take rubuta “LAA ĆAA’ATA LIMAKHLUĆIN FII MA’ASIYATIL KHALIĆI.” A dukkan kadarorinta data Mallaka, irin su motoci da sauran su, Tun farkon kafa kungiyar har zuwa yau dinnan kungiyar bata chanza ba.Haka kuma ta ko wacce fuska tarihin izala zaizo dogo ko gajere, ba za a taba mantawa da irin gudummar da marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ya bada ba wajen kafa wannan kungiya mai tarin albarka ba.Hakazalika Tarihin IZALA bazai kammala ba tare da an ambaci Marigayi Sheikh Isma’ila Idris Ibn Zakariyya (Shugaban Majalisar Malamai na farko) da irin gudunmawar da ya bayar dan kafuwar wannan kungiya mai albarka, da irin Su Marigayi Sheikh Ibrahim Bawa Maishinkafa, Marigayi Sheikh Hudu Chikaji Zariya, Marigayi Sheikh Adam Mai Shafi, Marigayi Sheikh Abubakar Imam Ikara, Marigayi Sheikh Musa Maigandu Muhammad, Marigayi Alhaji Ali Ibrahim Tofa (Tsohon Shugaban yan agaji na kasa), Marigayi Sheikh Rabi’u Aliyu Daura, Marigayi Sheikh Dr. Alhassan Sa’id Adam Jos, marigayi Sheikh Adamu Aliyu maigora, marigayi Sheikh Rabi’u Aliyu Daura, marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam koda Kuwa ba manufarmu mu zayyana sunan kowa ba.Suma sauran Matasan Malaman da a baya suka bada Gudunmawar su dan kungiyar ta cimma manufofinta, wanda a yanzu sun zama Dattawa, a farkon tafiya gashin su baki ne, amma yanzu ya rikide ya zama fari sol, kuma ba’a daina yin wa’azin ba, irin su Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina, (Trustee) na kungiyar, wanda a farkon tafiya shine Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai na biyu, Sheikh Usman Isah Taliyawa Gombe, Sheikh Abbas Muhammad Jega, Alaramma Abubakar Adam Katsina da Sheikh Habibu Yahaya Kaura wanda ake masa lakabi da dan autan masu wa’azi, sabo da kankantar sa, gashi yanzu shekaru sun cimmasa, da sauran wadanda suke raye ake fafatawa da su a halin yanzu irin su Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe, Sheikh Abubakar Giro Argungu, da dai sauransu.Daga karshe Muna addu’a ga dukkan wadanda suka sadaukar da dukiyoyin su da kuma rayukansu akan wannan harka taci gaban addini, Allah ya saka musu da gidan Aljanna ya hada mu dasu a babban matsayi a lahira. Amin.jibwisnigerian@gmail.comWANNAN SAKO NE DAGA KWAMITIN YANAR GIZO TA KUNGIYAR IZALA TA KASA, (JIBWIS SOCIAL MEDIA).JIBWIS NIGERIA đłđŹCC:Abdullahi Bala Lau Muhammad Kabir Haruna Ibrahim Baba Suleiman Jibwis Nigeria
Leave a Reply