Salman Rushdie, marubuci dan Indiya da rubutunsa ya kai ga barazanar kisa daga gwamnatin Iran a shekarun 1980, an caka masa wuka a lokacin da yake shirin gabatar da lacca a kudu maso yammacin jihar New York.
Yan sanda sun tabbatar da cewa an caka wa Rushdie wuka a sau daya a wuya kana sau daya a cikinsa a ranar Juma’a bayan da wani mahari ya yi zafin naman farmakarsa a kan dandali
Bayan an dauke shi a jirgin sama zuwa asibiti inda ya shafe sa’o’i a dakin tiyata, Rushdie yana kan na’urar numfashi kuma ya kasa magana tun da yammacin Juma’a, Al-Jazeera ta ruwaito.
Andrew Wylie, wakilin littafinsa, ya rubuta a sakon imel da ya aikawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa
“Mummunan labari ne, da alama Salman zai rasa ido daya; jijiyoyin hannunsa sun yanke; kuma an caka masa wuka ta taba hantarsa kana ta lalace.”
Yan sanda sun bayyana wanda ake zargin da wannan hari da suna Hadi Matar mai shekaru 24 daga Nevw Jersey.
Yan sanda sun bayyana wanda ake zargin da wannan hari da suna Hadi Matar mai shekaru 24 daga New Jersey.
Manjo Eugene Staniszewski na ‘yan sandan jihar New York ya shaidawa manema labarai a yammacin ranar Juma’a cewa jami’ai ba su da wata alama ta bincika tsuhen manufar Matar, sun dai ce ya yi radin kansa ne na sheke Salman.
Stacey Schlosser, wacce ta shaida harin, ta shaida wa kamfanin dillancin labaran AP cewa an caka wa Rushdie wuka sau shida zuwa takwas kafin a kama maharin.


Leave a Reply