Masha Allah – Afakallahu Zaiyi WUFF! Da Rukayya Dawayya

Shugaban Hukumar Tace Fina Finai Na Jihar Kano, Isma’il Na Abba (Afakallahu) Zaiyi WUFF! Da Jaruma Rukayya Dawayya, Tun Kwanakin Baya Muke Jin Kishin Kishin Din Soyayyarsu Inda Ake Cewa Afakallahu Zai Aureta,

Yanzun Dai Lamarin Ya Tabbata, Inda Dakanta Ita Rukayya Umar Santa Wacce Akafi Sani Da (Rukayya Dawayya) Tare Da Angon Nata Su Wallafa Katin Gayyatar Auren Nasu, Wanda Za.ayi Shi Farkon Watan 11 Wato Waton November.

Za.a Daura Auren Nasu Ne Ranar Jumma’a Wanda Yayi Dai Dai Da 4 Ga Watan Sha Daya Shekarar Dubu Biyu Da Ashirin Da Biyu. Misalin Karfe 2 Na Rana, Wato Bayan Sallar Jumma’a Kenan. A Masallacin Jumma’a Na Tishama Wanda Yake Cikin Garin Kanon Dabo.

Muna Fata Allah Yasa A Daura Auren Lafiya Ya Basu Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali Amin.