Masha Allah Ahmad Ali Nuhu yafara Buga kwallo tare da Turawa a kasar Turai
Babban dan Ali Nuhu mai suna Ahmad Ali Nuhu atun hirar da gidan jarida na BBC Hausa sukayi dashi kwanaki yace ya hakura da sana’ar film inda yace harkar kwallon kafa kawai zai koma a ita yake son yaci abincinsa.
Ana tsakiya da haka kuma sai mahaifinsa ya dauke shi ya kai kasar Ingila domin ya shiga makarantar koyon kwallon kafa domin ya koya shima wata ya buga a wata kungiyar ta Turawa.
Yanzu haka dai yaron yana kasar Ingila wanda cikin hukunci Allah harya samu damar yin atisaye da karamar kungiya achan kasar Turai din
An taya jarumi Ali Nuhu murnar samun gurbi da dansa yayi achan kasar ta Turai wanda hakan ba karamin abin alfahari bane a wajen Ali Nuhu da kuma kannywood gaba daya
An bayyana jajircewar mahaifin yaron ce ta kaishi wannan matakin da kuma shima yadda yasa abin acikin ransa muna masa addu’ar Allah ya kama masa

Leave a Reply