Matar Aure Ta Mutu Bayan Haihuwar Yan Uku A Sansanin Yan Gudun Hijira, Mijin Ya Bita Bayan 40
Allah ya yiwa wata matar aure rasuwa bayan ta haifo kyawawan yaranta guda uku a wani sansanin yan gudun hijira da ke jihar Borno.
Sai dai kuma yaran sun zama cikakkun marayu domin mahaifinsu ma ya kwanta dama kwanaki 40 bayan rasuwar mahaifiyar tasu.
Wannan al’amari ya taba zuciyar dan marigayi tsohon ministan Najeriya kuma dan siyasar Borno, Shettima Ali Monguno.
Borno – Wata matar aure ta rasu bayan haihuwar yan uku a sansanin yan gudun hijira da ke jihar Borno.
Rahma Monguno, dan marigayi tsohon ministan Najeriya kuma dan siyasar Borno, Shettima Ali Monguno, wanda ya bayyana hakan a ranar Juma’a, 23 ga watan Satumba, ya ce mijin matar ya bita bayan kwanaki 40 da rasuwarta.
Allah yasa mudace duniya da lashira ameeee summa ameen

Leave a Reply