Mijina baya iya biyamin bukata lokacin saduwa shi yasa ya rabu da uwar gidansa kafin ya auro ni, cewar wata Mata

Assalamun alaikum Malam mace ce mijinta ba ya iya biya mata bukata sabida raunin mazakutarsa sannan kuma ashe abin da ya raba shi da uwargidansa kenan Kasancewar ba ya biya mata bukata ta shiga cikin halin
damuwa.

Sannan ta yanke shawarar cewa: In ya kira ta shimfidarsa bata zuwa to malam ta yi laifi game da wannan shawarar data yanke a gare ta.

Wa alaikum assalam: A shawarata kamata ya yi a kira magabatansu su zauna su tattauna a gano yadda za’a warware matsalar Idan har ya tabbata ba cikakken Namiji ba ne to za’a ba shi shekara daya ya nemo magani.

Idan ya warke shikenan in bai warke ba kuma zata iya fadawa cikin haram idan ta cigaba da zama da shi, to ya halatta a raba auran kamar yadda aka raba da uwargidan na sa ta farko.

Yana daga cikin manyan manufofin aure: Ma’aurata guda biyu su katange junansu daga haram, in har aka rasa wannan to akwai matsala a zamantakewar aure na su.

Ya kamata duk masu mata da irin wannan matsalar su nemi magani domin samin zaman lafiya a zamantakewar auren su, wanda neman maganin zai iya kawo karshen matsalar da take addabar su.

Sannan hakan yana kara dankon soyayya a tsakanin Ma’aurata, domin idan kana neman maganin da zai kaudama wannan matsalar tabbas zakyi zaman lafiya kai da Iyalin ka.