Ministan Najeriya, Pantami Ya Ajiye Tarihi, Ya Yi Abin da Babu Wanda Ya Yi a Afrika

Isa Ali Ibrahim (Pantami) ya samu shaidar CIISec bayan yi masa jarrabawowi da gwaji
.  Ministan sadarwan yana da shaidar zama kwararre kan harkar tsare kafofin yanar gizo
.  Pantami ne mutumin farko a Afrika da ya samu wannan dama, mutum 89 ke da CIISec

Farfesa – Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali Ibrahim (Pantami) ya samu lambar zama ‘dan kungiyar Chartered Institute of Information Security.

Vanguard ta kawo rahoto cewa Farfesa Isa Ali Ibrahim (Pantami) ya samu wannan lamba ne biyo bayan wasu jarrabawowi da kungiyar tayi wa Mai girma Minista.

Kamar yadda cibiyar mai bada lambar girman ta bayyana, ana bada CIISec ne ga jagororin da suka yi fice wajen harkar tsaron bayanai da kafofin yanar gizo a Duniya.

mobile  media crew ta fahimci Isa Ibrahim wanda aka fi sani da Pantami ya samu shaidar CIISec, hakan na nufin ya zama cikakken kwararren ‘dan kungiyar tsaron yanar gizo.

Pantami ya bi sahun mutane 89
Rahoton Sun yace Ministan tarayyan ya zama mutum na 89 a Duniya da ke da wannan shaida, na farko a fadin nahiyar Afrika da ya taba samun shaidar CIISec.

Mutum yana samun CIISec ne idan ya yi fice a bangaren tsaron yanar gizo, baya ga haka ya nuna kokari wajen bunkasa wannan harka da yanzu ake ci da shi a ko ina.

A shekarar 2018 aka kirkiro da wannan lamba a kasar Birtaniya domin a karrama kwararrun masana.

Bayanan da ke shafin yanar gizon wannan kungiya ta Duniya ya nuna Farfesa Isa Ali Ibrahim ne kadai wanda ya fito daga kasar Afrika wanda aka san da zaman shi.

Hakan zai kuma ba Ministan dama wajen tantance sababbin wadanda za a ba wannan lambar girma, tare da iya aiki manyan gwamnatoci, kwararru da kungiyoyi.

Karin matsayi a kan matsayi
Isa Pantami ya samu shaidar CIISec ne kusan shekara daya bayan jami’ar fasaha ta tarayya da ke garin Owerri ta kara masa matsayi zuwa cikakken Farfesa a fanninsa.

Wannan karin matsayi da aka yi wa malamin a lokacin da yake aikin Minista ya jawo surutu. Kungiyar ASUU ta malaman jami’an ta nesanta kanta daga matsayin.