Momo ya sha ihu a kasuwa bayan amshe N10,000 da ‘Dan-ga-ruwa’ ya biya shi na barnar da ya masa

Jarumi Aminu Sheriff, wanda aka fi sani da Momo ya sha ihu a kasuwar singa da ke Kano bayan wani ya yi masa barna a motarsa.

Wani bidiyo wanda Tashar Tsakar Gida ta wallafa ya nuna yadda jarumin ke kirga kudi N10,000 a cikin kasuwa yayin da jama’a su ke yi masa ihu.

Kamar yadda aka gani, ya na sanye ne da babbar riga da hula yayin da wani da ake zargin mai tura kurar ruwa ne ya mika masa kudin ya amshe, ya kirga, sannan ya zuba a aljihu.

An ga yadda aka fasa masa kwalbar fitilar motarsa inda ake zargin hakan yasa ya tsaya tsayin-daka har sai an biya shi.

Bayan ya amshe kudin ya shige mota ne aka dinga yi masa ihu yayin da wasu ke kiransa da “Dan wahala”.

Lamarin ya fusata matasan wadanda da alamu su na kallon kamar ya fi karfin amsar kudin kuma ko da ma yana da bukatar, bai dace ya amsa a hannun dan-ga-ruwa ba.

Ya sha ihu kwarai kuma da alamun ko a jikinsa don ba tare da ya nuna bacin rai ko kuma ya mayar wa da kowa martani ba yayi shigewarsa mota ya tsere.

News All.