Babbar jaruma kuma jigo a masana’antar Kannywood Hajiya Hauwa Garba wadda akafi sanin ta da suna “Yar Auta ko kuma Sabira a cikin shirin nan mai dogon zango na Gidan Badamasi wanda Falalu A Dorayi yake bada umarnin shi.
Jarumar ta fito ta bayyanawa duniya wasu abubuwa game da ita a hirar da sukayi da gidan jaridar BBC Hausa.
Ta fadawa duniya abubuwan da suka shafi Rayuwar ta da kuma auren Marigayi Rabilu Musa Dan Ibro da tayi,harma da dalilin rabuwar su.
Sannan ta nuna ainihin yadda take gudanar da sana’ar ta ta fim musamman yadda take cancada kwalliya wadda babu mai yin irinta a duniya sai ita kadai.
Zaku iya kallon cikakken bidiyon ta hanyar danna hoton bidiyo dake kasa 👇👇