Nakashe Babana Da Mamana saboda Suna Ceman Mahaukaci

Labarai

Na Kashe Iyayena Saboda Suna Kirana Mahaukaci Don Ina Yabon Manzon Allah ~ Mawakin Tijjaniya Azzakiru Munkaila Rahoton NewsAll Hausa Matashin da ya kashe iyayensa a jihar Jigawa, Munkaila Ahmadu, ya bayyana dalilin da yasa ya hallaka iyayen da suka haifeshi da tabarya a karamar hukumar Gagarawa. Munkaila wanda Azzakiru ne, mawakin darikar Tijjaniyya yace iyayensa na kiransa mahaukaci kuma suna kalaman nuna rashin yarda da wakokin yabon Manzon Allah (SAW) da yake yi NewsAll ta ruwaito cewa Munkaila ya yi bayani a faifan bidiyo cewa ko kadan ba ya nadaman abinda yayi saboda ya yanke musu hukuncin wanda ya zagi Manzon Allah ne. A cewarsa: “Na kashesu ne saboda sun ki amincewa da gaskiya game da Manzon Allah (SAW). Na kashesu saboda hukuncin duk wanda ya zagi Manzon Allah kisa ne, kuma babu gafara ga wanda yayi haka.” “Na Azzakirun Manzon Allah, wannan shekarar nike da niyyar fito da bidiyon wakata kuma Idan Allah ya yarda zan yi hakan. Za’a sake ni saboda Allah na tare da mai gaskiya, shi yasa ko a jikina bana nadama.””Iyayena ba sa son Manzon Allah saboda ina yabonsa, sun ce ni mahaukaci ne, na roki mahaifi ne ya goya min baya, nace masa ba na neman mata, bana caca, ban shan kwaya, kuma ban sata, amma ya ki.” “Mahaifiyata har wajen makwabta take zuwa tana fadawa mutane ni mahaukaci ne saboda na kin zuwa gona.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *