RARARA YA CACCAKI GWAMNA GANDUJE A SABUWAR WAKAR DAYA FITAR LAMARIN DA YA HAIFAR DA CECEKUCE

Rarara ya tabbatar da cewa har yanzu shi Dan APC ne kuma Yana tare da tinibu da shattima Amma baya goyon bayan nasiru gawuna Dan takarar gwamna a APC Wanda ganduje yake fatan ya gajeshi mawakin daya shara wajen yiwa shigaba muhammadu buhari waka yayi ikirarin cewa ganduje ya bada umarnin cire sunansa daga kwamitin kamfen din takarar shugaban kasa.

An rawaito cewa mawakin baya goyon bayan nasiru gawuna Dan takarar gwamna a APC Wanda ganduje ya tsayar maimakon haka ya bayyana goyon bayan sa ga sha’aban Ibrahim sharada na jam iyyar ADP Amma ya bayyana cewa har yanzu na APC ne kuma Yana goyon bayan Dan takarar shugaban kasa tinibu da shattima .

Rarara ya kira ganduje da hankaka a sabuwar wakar da ya fitar ranar laraba don yiwa tinibu kamfen sannan kuma ya tabbatar da rikicin su da ganduje inda ya kirashi da hankaka ma ana me fuska biyu kenan rarara kuma ya zargi ganduje da dakile saka sunansa a kwamitin kamfen din shugaban kasa.
To Allah yasa mu dace AMIN.