Rukayya Dawayya Ta Koka Kan Yadda Yayan Masu Kudin Ke Auren Junansu A Kasar Nan

Shahararriyar jarumar Kannywood, Rukayya Umar Dawayya ta yi martani a kan yadda ake yin kwarya tabi kwarya wajen kulla auratayya a kasar nan.

Dawayya ta shawarci ya’yan talakawa da ke da kyau a kan su daina yarda da soyayya tsakaninsu da yaran masu kudi domin magana ta gaskiya ba auransu za su yi ba.

A cewarta koda yaran na son su iyayensu ba za su amince a kawo masu diyar talakawa a matsayin suruka ba, don haka ta shawarce su da su tashi su nemi ilimi don gobensu.

Jarumar fim din tayi misali da abun da ke faruwa a kasar yanzu haka inda tace duk auren da ake yi a yanzu tsakanin ‘yar wane da dan wane ne.

A cewarta ta haka ne za a samu arzikin ya kai gidan kowa amma masu kudin sam basa kaunar ganin haka.

Don haka ta shawarci ‘ya’yan mallam shehu wato talakawa da su dage da neman ilimin addini tunda har na Bokon ana so a hana suyi sakamakon yajin aikin da ake zuwa.

Wani bangare na jawabin nata na cewa:

“Wani abu ne yake damuna kullun idan na ga abun nan sai ya tsayamun a raina. Kun ga yaran nan zuwa nayi na baku shawara, ya’yan mallam Shehu yan uwana, ya’yan talakawa billahillazi ku kama kanku, kun ga kuna da kyau kuna da wayewa, ‘ya’yan masu kudi da suke zuwa suke karya suna soyayya da ku wallahi amfani suke yi da kyau da kuruciyarku babu dan mai kudin da zai iya zuwa gidan babansa ya kai sunanki wai zai aure ki.

“Wai dan Allah baku lura da abun da ke faruwa bane yasu-yasu suke haduwa suke aure, jama’a wannan wani irin rashin kara ne kuke mana masu kudin kasar nan? Da me za a ji ai sai ana aurataitaniya a tsakani sannan za a samu arziki ya shiga gidan kowa. Yar talaka ta auri dan mai kudi, yar mai kudi ta auri dan talaka duk wanda ya ga wanda yake so a bashi amma sai ki ga ango zukeke kamar shi yayi kansa matarsa kamar a yanka a boye wuka don muni amma ya aureta saboda yar wani ce.

News All