Safara’au Yadda video din tsaraicina ya fito da kuma wanda suka fito dashi

A wata hira da shafin BBCHausa sukayi da mawaki Safara’u wanda akafi sani da SAFA ta bayyana yadda bidiyon tsiraicinta ya fita yabi duniya.

Amihad.com ta kawo muku yadda ta kasance da kuma cikakken bidiyon hirar da tayi da majiyar tamu.

Kamar yadda kuka sani a watannin baya ne bidiyon tsiraicin Safara’u, mai fitowa a shirin Kwana Casa’in da Arewa24 ke shiryawa, ya fita duniya.

Wanda bayan fitar bidiyon, masu shirya fim din sun dakatar da ita daga shirin lamarin da ya sa ta tsunduma cikin harkokin wakoki.

BBCHausa ta rawaito cewa Safara’u ta bayyana yadda aka yi bidiyon ya fita a duniya da kuma wadanda take zargi da fitar da shi. Matashiyar ta ce ta shiga mawuyacin hali bayan faruwar lamarin inda ta kai har wata uku ba ta fita ko waje ba, har ma ta kai ana jifan ta da duwatsu idan ta zo wucewa ta wani wuri.

Kazalika cikin wannan hira da majiryar tamu tayi da ita mawakiyar ta bayyana irin hakin da ta shiga bayan fitar wannan bidiyo.

Ta kara da cewa mutane da yawa sun ce tayi abin ne domin tura wa wata kawarta da suke madigo tare inda wasu kuma ke cewa ta aika wa saurayinta bidiyon ne.

Sannan cikin bdiyon tace: ‘‘Na kan yi irin wannan bidiyo na ajiye a wayata saboda jin dadi ko na wani abu daban, kuma ni na sani kashi 70 cikin 100 na mata na irin wadannan bidiyo su ajiye a wayoyinsu”, in ji Safara’u.

Ga dai cikakken bidiyon hirar da akayi da ita nan sai ku kalla domin jin ta bakinta.