w
Malam Ibrahim Shekarau, ya bayyana yadda Sanata Rabiu Kwankwaso, ya yaudare shi da ma magoya bayansa bayan da ya jawo su zuwa jam’iyya mai kayan marmari ta NNPP a watan Mayu.
Shekarau da Kwankwaso dukkansu tsoffin gwamnoni ne a Kano, jiha mafi tashen kasuwanci a Arewa maso Yammacin Najeriya, Leadership ta ruwaito.
A yau Litinin, 22 ga watan Agusta, Shekarau ya shaida wa manema labarai cewa, zai bayyana matsayinsa na yiwuwar sauya sheka da NNPP zuwa wata jam’iyyar nan ba da jimawa ba.
A halin yanzu, Shekarau ne wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar dattawa kuma tsohon jigo ne a jam’iyyar APC mai mulki, rahoton Tribune Online.
Nan kusa zan fadi matsaya ta
Da yake bayani ga manema labarai,ya ce ya gana da kwamitinsa na Shura a karshen mako, inda suka tattauna kan batutuwan da suka shafi makomai siyasar Atiku Abubakar da kuma yiwuwar komawar Shekarau PDP.
Barista Habib Shehu, wanda shine jagoran kwamitin na shura an ce ya ba da rahotonsa domin duba da kuma yanke shawarar karshe.
Ya zuwa yanzu dai Shekarau bai bayyana PDP zai koma ba, amma ana ta rade-radin tawagar Atiku na bin kafa domin zawarcin jigon siyasar zuwa PDP.

Leave a Reply