Tabbas Nayi Zina Da Ita Amma Ba Nina Mata Ciki Ba – Yaya Ga Kanwarshi

Wani magidanci ne matarsa ta haihu, duba da halin da matar take ciki sai iyayenta suka turo mata kanuwar ta domin ta kula da ita har izuwa lokacin da jikin nata zai warware, amman zai akayi rashin nasara mijin shi wannan matar ya lallaba ya dirkawa ita kanuwar ma ciki.

Bayan hakan ta bayyana har ya kai izuwa ga manya sun shiga maganar, duk da haka bai amsa cewa laifin nashi bane, iya abun da ya amsa shime, wai shi dai ya san cewa ya kwanta da ita har sau uku amman wannan ciki dai gaskiya ba nashi bane.

Haka dai yayi ta banbani cewa wai shi cikin nan dai ba nashi bane, har yana qalubalantar su wai cewan aje asibiti a yi gwaji, indai ya tabbata cikin nashi ne to fa zai karba inko ba nashi bane to bazai karba ba.

Ita kuwa kanuwar matar ta ce lallai shine domin yun zuwanta gidan yake bibiyar ta, da farko ma bayan zuwan ta gidan a dakin yayar tata take kwana amman daka baya shine yace mata wai ta koma dakin baki shine zaina kwana da matar tasa

Ashe manufarshi shine ya dinga samun dama daga ita sai shi.. yanzu gashi ina amfanin wannan abin kunyar, ace ka yima mata da kawa ciki su biyu ai wannan bai kamata ba.

Allah ya sa mu cigaba da fin qarfin zuqatan mu, mu kuma dinga kiyayewa abubuwan da basu da kyau. AMEEN.

News All